GUGUWAR ƘARIN KUƊIN FETUR: Dillalan mai na bin gwamnatin tarayya bashin naira biliyan 100 -Shugaban NMDP, Ahmed Faruk

Sabon Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai (Midstream da Downstream), Ahmed Faruk, ya ce dillalan mai da masu dakon mai na bin gwamnatin tarayya bashin naira biliyan 100.

Da ya ke magana da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ganawar su da Shugaba Muhammadu Buhari, Faruk ya ce bashin ya taru ne tun daga 2017 har zuwa cikin Oktoba, 2021.

“Kun san ba a daɗe da naɗa ni kan wannan muƙami ba. To da na hau sai na gano tulin takardun da ke nuna masu dako da dillalan fetur na bin gwamnatin tarayya bashin naira biliyan 100, waɗanda su ke bi tun daga 2017 har zuwa cikin Oktoba, 2021.

“To amma mu na nan mu na tantancewa, kuma za a biya su kuɗaɗen su.

“Sai dai ya na da kyau a sani cewa na gaji bashi har na naira biliyan 100 kenan.”

Faruk ya yi ganawa da Buhari da kuma Karamin Ministan Fetur, Timipre Sylva, sai kuma Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Fetur (NUPRC), Gbenga Komolafe.

Ƙarin Farashin Mai Zuwa Naira 340:

Bayan jawabin da Ministar Harkokin Kuɗaɗe ta yi kan cire tallafin mai, Hukumar NNPC ta bayyana cewa cikin shekarar 2022 litar mai ɗaya za ta iya kai naira 320 ko ma naira 340.

Shugaban Hukumar NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana haka a ranar Talata.

Gwamnatin Buhari za ta tsula farashin litar fetur, amma za a rika bai wa talakawa naira 5000 su rage raɗadin ƙuncin rayuwa.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta cire kuɗin tallafin man fetur, wanda hakan na nufin za a ƙara kuɗin litar fetur.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, a lokacin ƙaddamar da wani shiri na Bankin Duniya a Najeriya.

Sai dai kuma ta ce gwamnatin tarayya za ta zaƙulo mutane miliyan 30 zuwa 40 da su ka fi kowa talauci a kasar nan ta riƙa ba su naira 5,000 kowace Wata, domin rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwar da za su iya afkawa a ciki nan gaba idan an ƙara wa fetur farashi.

Ta ce rarar kuɗaɗen da za a riƙa samu ce za a duba sannan a san ko adadin mutum nawa ne za su riƙa amfana da tallafin.

Idan ba a manta ba, Bankin Bada Lamuni na Duniya, IMF ya shawarci Najeriya ta gaggauta cire tallafin mai domin ta ƙara samun kuɗin shiga. Kuma ta rage kashe kuɗaɗe a ayyukan da ba masu muhimmanci ba.

Bankin IMF ya shawarci Najeriya ta gaggauta cire tallafin da na kuɗin wutar lantarki a farkon 2022.

Idan Gwamnatin Najeriya ta yi amfani da shawarar Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) har ya cire tallafin man fetur da na wutar lantarki a farkon 2022, ‘yan ƙasar nan za su shiga sabuwar shekara cikin halin ƙuncin rayuwar da ta fi ta shekarar 2021 da ake ciki.

Kai tsaye ba wani abu ba ne cire tallafin man fetur da na wutar lantarki, ma’ana ita ce a ƙara wa farashin litar man fetur da wutar lantarki kuɗi.

IMF ta gargaɗi Najeriya cewa yawan kuɗaɗen da ta ke kashewa idan auna su da waɗanda ta ke samu, to za’a ci gaba da samu wawakeken giɓi a kowace shekara, kamar irin wanda aka samu a bana cikin 2021, to haka ma za ta kasance a shekara mai zuwa.

“Amma idan aka cire tallafin fetur da na kuɗin lantarki, an kamo hanyar saisaita matsalolin ƙaranci kuɗi a hannun gwamnati kenan.

“Amma kuma tilas sai ita gwamnatin ta bijiro wasu tsare-tsaren da za ta rage wa talakawa tsadar rayuwa, sakamakon matsin da za su shiga idan an ƙara kuɗin fetur da kuɗin wutar lantarki. Kuma dama akwai wannan sharaɗin a cikin Sabuwar Dokar Man Fetur ta 2021 cikin watannin baya.”

IMF ya ƙara da cewa, tafiyar-hawainiyar da sabon tsarin canjin kuɗaɗe ke yi, tare da rashin tabbas na kasa maido maƙudan kuɗaɗen da ɓarayin gwamnati su ka sace suka ɓoye a waje, ya rage ƙarfin yawan shigowar jari mai nauyi a Najeriya.”

Wasu ƙarin matsalolin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da fuskanta, a cewar IMF, sun haɗa da ƙarancin kayan da Najeriya ke fitarwa waje.

A kan haka sai IMF ta nemi Najeriya ta fito da wani tsari da zai daɗe tsawon lokaci ya na hana kuɗaɗen ajiyar Najeriya a waje raguwa.