Ghana Za Ta Hana Shiga Da Shinkafa Da Wasu Kayayyaki Cikin Kasar

Ministan ciniki da masana’antu, Kobena Tahir Hammond, ya sanar da wani muhimmin mataki da gwamnatin Ghana ta dauka na samar da dokar hana shigowa da kayayyaki sama da 20, ciki har da shinkafa da wasu kayayyakin da ake amfani da su a Ghana.