GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

Ƙwallon da za a buga yau a birnin Kumasi na Ghana tsakanin Ghana da Najeriya, yaƙi ne wurjanjan guda uku za a kafsa, a lokaci ɗaya, kuma a cikin mintina 90.

Duk wanda ya yi nasara, to ya share wa kan sa hanyar zuwa Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022. Idan Ghana ta yi nasara, to ta ƙara yi wa Najeriya nisa wajen tarihin yawan yin nasara a kan ta.

Idan Najeriya ta yi nasara, to ta ƙara kankaro kan ta daga gorin da ‘yan Ghana ke yi mata, cewa sun fi Najeriya yawan yin nasara a karawar su da juna.

Sannan kuma a gefen barkwanci, ‘yan Najeriya da ‘yan Ghana na cewa duk wanda aka ci a yau, to kawai ya haƙura an fi ƙasar iya dafa lafiyayyar shinkafa ‘jallof rice’ kenan.

Tarihin Yadda Ghana Ta Riƙa Kunyata Najeriya A Wasan Kwallo:

Najeriya da Ghana sun fara kafsawa tun a cikin 1950. Amma rabon su da haɗuwa a baya bayan nan tun cikin 2011.

Ƙasashen biyu sun taɓa haɗuwa har sau 56. Karawar da za a yi a Kumasi yau Juma’a, za ta kasance ta 57.

Ghana ta yi nasara kan Najeriya har sau 25, sun yi kunnen-doki sau 19, Najeriya ta yi nasara sau 12 kacal.

Sau 16 Najeriya na zuwa Ghana ta dawo da lodin buhun kunya gida. Sau 6 ta yin kunnen-doki a Ghana.

Karawar baya-bayan nan da aka yi sau biyar, an canjaras a 2011 a Ghana, an yi 1:0 a kan Najeriya a Ghana ciki 2010. Sannan a 2008 an ci Najeriya 2:1 a Ghana. Cikin 2007 an ɗura wa Najeriya ƙwallaye 4:1 a Ghana. A 2006 ne Najeriya ta yi nasara 1:0 a gida.

Yayin da Ghana ba ta samu halartar cin Kofin Duniya na 2018 ba, ita kuwa Najeriya sau huɗu kenan ta na zuwa a jere, babu fashi.

Bayan karawar da za a yi a ranar yau Juma’a a Kumasi, a 29 za a kara karo na biyu a Najeriya. A ranar za a gane mai tafiya Qatar 2022 da wanda zai zauna gida ya ci gaba da cin ‘jallof rice’ ɗin sa garau garau.