Ghali Na’Abba ya ɗora laifin matsalolin ƙasar nan kan masu mulki

Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na’Abba ya ce matsawar shugabannin ƙasar nan a matakan sama har zuwa ƙasa ba su ɗauki riƙon amanar shugabancin jama’a da muhimmanci ba, to Najeriya ba za ta taɓa tsallake siraɗin ƙalubalen da suka dabaibaye ta ba.

Ghali ya ɗora laifin matsalar koma-bayan tattalin arziki da rashin tsaro a kan manyan shugabannin siyasa, ciki kuwa har da shi.

Ya ce duk waɗannan matsaloli da ake fama da su, sun assasu ne daga son rai da dogon-burin shugabanni.

“Akwai sakaci da rashin maida hankali. Su waɗanda ke kan mulki sun ƙi su karɓi gyaran da ake yi masu, har su dawo kan hanya miƙaƙƙa. Mun tafka asarar dimokraɗiyya kawai, saboda waɗanda ke tafiyar da ƙasa a ƙarƙashin mulkin dimokraɗiyya sun ƙi tsayawa su bi tsarin yadda ya kamata. Sun koma su na son-rai, shirme, badambadama da hauragiya har tsari da ingancin dimokraɗiyyar ya karye.

“Maganar gaskiya fa tilas a faɗe ta. Kasar nan sai ƙara dagulewa ta ke yi, saboda kawai mun duƙufa wajen ganin an cika wa wasu ‘yan tsiraru buri da muradan su.’

Ghali ya ce tilas sai an gyara daga sama har ƙasa kafin a ga komai ya daidaita.” Haka Ghali ya furta a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.

Ba tare da Ghali ya ware jam’iyyar sa PDP ba, ya ce tsarin siyasa da shugabancin ƙasar nan a siyasance kwamacala da cakwakiya ce danƙare da shi.

Ya nuna damuwa dangane da yadda gwamnoni ke yin kaka-gida a shugabancin jam’iyya da ƙarfa-ƙarfa kan ikon Majalisar Dokoki ta jiha zuwa Tarayya.

Ghali wanda ya yi Kakakin Majalisar Tarayya tsakanin 1999 zuwa 2003, ya nuna damuwar sa ganin yadda bai samu nasarar tsige tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ba, a lokacin da ƙalubalen siyasa ya tirniƙe a ƙasar nan.