GARGADI GA MASU CIWON HAWAN JINI: Ku kaurace wa magani ‘Norvasc’ yana da hadarin gaske – Mahukunta

Gwamnatin jihar Edo ta gargaddi mutanen jihar da su nisanta kansu daga amfani da kwayoyin maganin ‘Norvasc’ 5mg.

Norvasc magani ne da masu fama da hawan jini ke amfani da shi domin samun sauki.

Kwamishinan lafiya na jihar Obehi Akoria ne ta yi wannan gargadi a wata takarda da ta fitar ranar Laraba a garin Benin.

Akoria ta ce gwamnati ta yi wannan gargadi ne bayan hukumar kula da ingancin abinci da magani ta kasa NAFDAC ta bayyana cewa akwai hadari a cikin wannan maganin.

“NAFDAC ta fadi haka ne bayan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Taiwan ta kira a dawo da kwayoyin maganin guda miliyan shida da aka shigo da su daga kasan zuwa Najeriya.

“Kamfanin sarrafa magunguna Viatris Inc dake kasar Amurka ce ta ke hada maganin.

“ A dalilin haka gwamnati ta yi kira ga mutane, manyan shagunan siyar da magunguna dake ajiye da maganin Norvasc 5mg da su rabu da maganin ta hanyoyin da ya kamata.

Ta yi kira ga mutane musamman wadanda ke fama da hawan jini Kuma suke amfani da wannan maganin da su gana da likitocin su kafin su fara amfani da wani maganin hawan jinin.