GANGAMIN APC: Babu wani ɗan takara da na zaɓa daga cikin ƴan takara 23 na APC – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai bayyana sunan kowa ba a matsayin ɗan takarar da ya ke ya gaje shi a cikin jerin ƴan takara 23 dake neman maye gurbinsa idan wa’adin sa ya cika.
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya umarci gwamnonin Arewa wand ya gana da su cewa su koma su zauna tare da jam’iyyar domin a samu matsaya daya game da wanda za a fidda ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Lalong ya ƙara da cewa a ganawar sun nemi afuwar shugaba Buhari bisa matsayar da suka ɗauka na cewa mulki ya koma kudu ba tare da sun sanar da shi tun da farko ba.
Abubakar Bagudu ya ce” A ganin mu ya kamata a ce dai tunda Arewa ta yi mulki idan ta kammala sai ya koma kudu. Wannan shine muka ga ya fi dacewa kuma muka amince da shi.
Shi ko gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, cewa yayi bayan ganawar gwamnonin dukkan su sun amince da mulki ya koma kudu in banda gwamnan Kogi Yahaya Bello wanda ya ce bai amince da haka ba.
Buhari bai tsaida ɗan takara ba
Gwamna Abubakar Badaru na Jigawa ya ce har yanzu gwamnonin APC na Arewa na jiran Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana matsayar sa kan miƙa takarar shugaban ƙasa ga ɗan kudu kai-tsaye.
Badaru ya bayyana haka a cikin wata tattaunawar da ya yi da BBC Hausa a ranar Lahadi.
A ranar Asabar ce dai Gwamnonin APC na Arewa da masu faɗa-a-ji na jam’iyyar daga Arewa, su ka amince mulki ya koma kudu a zaɓen 2023. Wato dai APC za ta tsayar da ɗan takara kenan daga kudu.
Badaru wanda shi ma ya na cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa, ya ce har yanzu Buhari bai bayyana matsayar sa a kan amincewa ko rashin amincewa da hakan ba.
Badaru ya ce maganar gwamnoni Arewa sun amince, bai tayi ne su ka miƙa, ba a kai ga daddalewa ba tukunna.
Badaru ya ce ya yi mamakin da ya ji “wai an raba takardar bayan taro mai ɗauke da sa hannun mutane, wadda a maganar gaskiya ba haka abin ya ke ba.
“Mu tayi ne mu ka miƙa wa Baba Buhari, idan ya ga hakan ne mafita kuma ya amince, shikenan, sai a yi hakan. Idan kuma bai amince ba, sai mu ci gaba a kan tsarin da mu ke. Amma dai mu gwamnonin Arewa mu ka goyon bayan duk wata matsaya da Buhari ya bijiro da ita.”
Ya ce Gwamnonin Arewa sun wakilta Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi da Simon Lalong na Filato da Abdullahi Sule na Nasarawa su je su sanar wa Shugaba Buhari cewa sun yarda duk ɗan Arewa mai takara a APC, to ya janye a bar wa ‘yan kudu su fito da ɗan takara a cikin su.
“Gaskiya ne Gwamnonin Arewa kamar su 11, ciki har da Ni mun tattauna wannan batu, sannan mu ka aika wa Shugaba Buhari cewa mun yi la’akari da halin da ake ciki, saboda haka mun yarda a bai wa ‘yan kudi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC.”
“Maganar janyewa ta kuwa, ba za ni yi gaggawar janyewa ba, har sai na ji matsayar da Shugaba Buhari ya fitar.”
Wato dai kenan har yanzu dukkan ‘yan takarar 23 kowa na ciki, ko ɗaya bai janye ba.