Ganduje ya naɗa sabon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Barista Mahmud Balarabe, a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar karban ƙorafe-ƙirafe da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

Barista Balarabe wanda a halin yanzu Darakta ne a Ma’aikatar Shari’a ta jihar, shi zai ci gaba da gudanar da ragamar hukumar a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun Babban Sakataren yaɗa labarai na Gwamnan Jihar, Abba Anwar.

A cewar sanarwar, naɗin ya fara aiki ne nan take.
Gwamnan ya umarci mukaddashin shugaban hukumar da ya gudanar da ayyukansa bisa tsarin yadda aka kafa hukumar.

Naɗin ya biyo bayan dakatar da shugaban hukumar ta yaƙi da cin hanci da rashawa Barista Muhyi Magaji Rimin Gado da majalisar dokokin jihar Kano ta yi.