Fitacciyar Jaruma kuma mahaifiyar Jarumai Zainab Booth ta rasu

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Rahotanni daga masana’antar Kannywood a jihar Kano na bayyana rasuwar Hajiya Zainab Musa Booth, fitacciyar jaruma da ta daɗe tana fitowa a fina-finai kuma mahaifiyar jarumai Ramadan Booth, Amude Booth da Maryam Booth.

Marigayiyar ta rasu a daren jiya Laraba kamar yadda rahotonnin suka nuna.

A kwanakin baya aka yi wa Hajiya Booth tiyata a zuciya wadda aka bayyana cewa an kammala aikin cikin nasara.

Za a yi jana’izanta da safiyar yau da misalin ƙarfe 8 a ƙofar gidanta dake kallon asibitin Premiere na kan titin Court Road a cikin birnin Kano.

Hajiya Zainab kusan za a ce da ita aka buɗe Kannywood kuma ta fito a manyan fina-finan Hausa da ma na turanci da masana’antar ta yi a baya-bayan nan.