FIDDA-GWANIN PDP 2023: Tambuwal ya janye ya ce ya na bayan Atiku

Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya janye takarar shugaban ƙasa a wurin gangamin taron zaɓen fidda gwanin PDP, ya ce ya na goyon bayan Atiku Abubakar.
Tambuwal wanda ke cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa 15 bayan janyewar wasu uku, ya yi kira ga magoya bayan sa su zaɓi Atiku Abubakar.
A yau ne ake ƙwama zaɓen fidda-gwani na PDP a Babban Filin Wasa na Ƙasa da ke Abuja.
Bayan janyewar Peter Obi da Hayatuddeen Mohammed da Nwachukwu Anakweaze, Tambuwal shi ma ya janye.
Idan an lura Tambuwal ya na fuskantar matsin lambar dusashewar hasken siyasar sa a cikin jihar Sokoto, tun bayan kisan Deborah, wanda Gwamnantin Sokoto ta yi Allah-wadai da kisan.
Zaɓen Fidda-gwani A Idon EFCC:
PREMIUM TIMES Hausa ta buga dalilin baza jami’an EFCC filin zaɓen fidda-gwanin PDP a Abuja.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa akwai dalilan da su ka sa ta baza jami’an ta a filin wasa na ƙasa, inda ake zaɓen fidda-gwanin PDP a cikin daren nan.
Kakakin EFCC Wilson Uwujaren ya tabbatar wa PREMIUM TIMES baza jami’an na su, kuma ya ce “mun je wurin ne don mu ga yadda gangamin taron zai kasance na yadda za a zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa.”
Da aka tambaye shi ko jami’ai nawa aka tura a Dandalin Gangamin, Uwujaren ya ce “a yanzu ba ni da adadin yawan su tare da ni.”
Dama dai Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Maina ya yi alƙawarin bin diddigin yadda jam’iyyun siyasa da ‘yan takara ke kashe kuɗaɗen su wajen kamfen, sayen fam da kuma zaɓen fidda gwani.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES Hausa ta lura da cewa EFCC ta kasa yin komai wajen yadda aka riƙa sayen wakilan zaɓen ‘yan takara a matakai daban-daban na zaɓukan faɗin ƙasar nan a cikin ‘yan kwanakin nan.
Wakilin mu kuma ya lura da cewa duk wani hoɓɓasa da EFCC za ta yi a yanzu, ba zai samu yabo daga idon ‘yan Najeriya ba, ganin yadda hukumar ta kasa taka wa jigon APC Bola Tinubu burki a zaɓen 2019, lokacin da ya ciki motoci biyu maƙil da kuɗi daga banki, a jajibirin zaɓen 2019, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar.
Sannan kuma a shekarar an yi ƙorafin cewa Gwamnatin Tarayya ta toshe ƙofofin yadda Atiku zai yi amfani da kuɗaɗe a lokacin kamfen, amma kuma EFCC ta ƙyale Tinubu ya jidi kuɗaɗe daga banki ya kai gida, domin biyan buƙatar cin zaɓe.
A zaɓen fidda-gwani na yau dai manyan ‘yan takara sun haɗa da Atiku Abubakar, Gwamna Nyesom Wike, Aminu Tambuwal na Sokoto, Bukola Saraki.