FARMAKIN GIDAN KASON JOS: An kamo fursinoni 21 daga cikin 252 da suka arce

A ranar Talata ne hukumar NCoS ta bayyana cewa ta kamo fursinoni 21 daga cikin 252 din da suka arce daga gidan kason Jos jihar Filato.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ASC Geofrey Longdiem ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Jos.
Shugaban hukumar NCoS Mohammed Tukur ya ce fursinoni sun arce ne saboda rashin kayan aikin zamani da suke fama da shi a gidan kason.
Longdiem ya ce NCoS ta hada hannu da sauran jami’an tsaro domin ganin sun kamo sauran fursinoni da suka gudu.
Ya ce wasu mutum biyu daga cikin fursinoni da suka gudu sun dawo da kansu sannan mahaifiyar wasu fursinoni biyu ta dawo da ‘ya’yan ta gidan kason.
Longdiem ya yi kira ga mutane da su hada hannu da hukumar ta hanyar sanar da jami’an tsaro a duk lokacin da suka ga wani fursina.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda fursinoni 252 suka arce daga gidan kason a Jos a dalilin farmakin da ‘yan bindiga suka kai a wannan gidan kaso.
‘Yan bindigan sun yi batakashi da jami’an hukumar NCoS dake tsaron wannan gida.
Kakakin hukumar Francis Enobore ya ce a dalilin harin mutum 10 sun mutu inda a ciki akwai ma’aikacin hukumar daya sauran kuma duk fursinoni ne da suka nemi gudu ta ritsa da su.
Sannan akwai mutum 6 da suka ji rauni a dalilin harin.
Ya ce hukumar ta kama mutum 10 daga cikin wadanda suka gudu kuma har yanzu ana farautar saura fursinoni 252 da suka gudu.