El-Rufai ya ayyana Litinin ranar jimamin rasuwar Bantex

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bada hutun ranar litinin ga ma’aikatan jihar domin yin jimamin tsohon mataimakin gwamnan jihar Barnabas Bantex.

Mai baiwa gwamna El-Rufai shawara kan harkar yaɗa labarai Muyiwa Adekeye ne ya sanar da hakaa madadin gwamna El-Rufai ranar Lahadi.

Muyiwa ya ce ba za ayi aiki ba ranara litinin domin jimamin rasuwar tsohon mataimakin gwamnan.

Gwamnan El-Rufai ya sanar da rasuwar tsohon mataimakin sa, Barnabas Bala Bantex a cikin wata doguwar sakon ta’aziyya da ya aika wa iyalan sa ranar Lahadi.

Bantext ya rasu ranar Lahadi, kamar yadda aka fidda sanarwar rasuwar sa.

El-Rufai ya bada tarihin marigayin tun daga lokacin da suka fara haduwa a jami’ar Ahmadu Bello a cikin 70’s.

” Tun a makaranta muna tare da Bantex, har muka gama. Sannan ko a ayyuka mun yi da yawa tare har na tsunduma ssiyasa. A nan ma muka yi takarar gwamna shi mataimakina tare kuma muka yi aiki tare har tsawon shekara huɗu.

El-Rufai ya kara da cewa marigayi Bantex mutumin kirki ne da jihar Kaduna za ta yi jimamin rashin sa.