‘Duk wanda muka samu ya haɗa baki da Nnamdi Kanu zai ɗanɗana kuɗarsa komai girman matsayinsa’, Gwamnati

Gwamnatin tarayya ta zayyana wa ƙasashen Turai laifukan da take zargin jagoran ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra ta (IPOB) Nnamdi Kanu da aikatawa.

Majiyarmu ta BBC ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ce Nnamdi Kanu ne ya kitsa kisan mutane 60 da lalata dukiyoyin jama’a a hare-hare 55 da aka kai a yankin Kudu Maso Gabas da Kudu maso Kudu a cikin watanni huɗun da suka gabata.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa wasiƙar wacce ke ɗauke da kwanan wata 26 ga Afrilu, 2021, ta yi bayani dalla-dalla kan ta’addancin da ake zargin mambobin kungiyar IPOB na aikatawa bisa umarnin shi Kanu.
NAN ta kuma ruwaito cewa daya daga cikin abubuwan da aka zayyana a wasikar har da hare-hare kan rayuka da dukiyoyin jama’a da kungiyar IPOB din ta kai wasu sassan kasar tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu 2021.
A gefe guda gwamnatin ta ce ba za ta ƙyale duk wanda ta kama da haɗa baki da shugaban na IPOB wajen ƙaddamar da hare-hare a kan jama’a ba, ‘’komai girman matsayinsa’’
Jaridar Vanguard ta rawaito ministan yaɗa Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana matsayin Gwamnatin Tarayyar a wani taron tattaunawa da manema labarai a Abuja da safiyar Alhamis.
Ministan ya ce tun shekaru biyu da suka gabata gwamnatin ke bibiyar Kanu wanda ke rayuwa ta ƙasaita a ƙasashe daban-daban, ciki har da zama a manyan hotel-hotel na ƙasaita da kuma yin tafiye tafiye a jirage masu zaman kansu.