DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

Shahararren ɗan wasan gaba na Real Madrid, Karim Bezema wanda aka yi wa ƙasaitaccen bukin bankwana bayan shafe shekaru 12 a ƙungiyar, yanzu dai ya dira a sabuwar ƙungiyar sa ta ‘Club Al-Ittihad’ da ke Saudi Arabiya, inda zai yi wasa na shekaru biyu kafin ya yi ritaya da buga ƙwallo ɗungurugum.

Kungiyar ta bayyana labarin dirar Benzema, kuma har ta yi masa kyakkyawar tarba, inda zai buga ƙwallon shekaru biyu, a kan jimillar albashin Naira biliyan 200,000 kenan.

Kwantiragin yarjejeniyar da Benzema ya rattaba wa hannu, ta yi nuni da cewa idan ɗan wasan ya ga dama, zai iya ƙara tsawon shekara ɗaya a ƙungiyar, kuma su lale masa Naira biliyan 100 ɗin sa.

Messi Ya Kama Hanyar Tafiya Amurka, Don Buga Wa Inter Miami Wasa Kafin Ritaya:

Shahararren ɗan ƙwallo Leonel Messi zai koma ƙungiyar International ta Miami da ke Amurka, bayan kammala wasan sa a PSG ta Paris, a ƙasar Faransa.

An yi tsammanin zai koma Barcelona, amma daga baya ejan ɗin sa ya tabbatar da cewa Messi Amurka zai koma ya ci gaba da wasa a kulob ɗin Inter Miami, mallakar fitaccen tsohon ɗan wasa, kuma ɗan ƙwalisa, David Beckam.

An yj tunanin Messi zai bi Benzema su riski Ronaldo a Saudiyya, inda N’Golo Kante da Zaha su ka rangaɗa a wannan kakar.