DA WANNE ZA AJI: Kwalara ta kashe mutum 75 cikin mako ɗaya a jihar a Katsina

A cikin Mako guda, cutar Kwalara ta kashe mutum 75 a jihar Katsina sannan kuma an samu mutum sama da 1500 sabbin kamuwa da cutar a jihar.

Kwamishinan Ilimin jihar Yakubu Danja ya bayyana cewa zuwa yanzu cutar ta yaɗu zuwa ƙananan hukumomin jihar 24 cikin 33 dake jihar.

Kwamishina ya kara da cewa ƙananan hukumomin
Funtua, Charanci, Kankara, Rimi, Sabuwa, Jibia da Kafur ne cutar ta fi tsanani a can.

” Bisa ga sakamakon binciken mu mun gano cewa kashi 67 bisa 100 na waɗanda suka kamu yara matasa ne ƴan shekara 15 zuwa sama sannan kuma maza ne suka fi kamuwa da ita kwalaran.

” Karamar hukumar Funtua ce ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar a jihar, Funtuwa na da mutum 384 yanzu haka da ke fama da kwayoyin cutar.

” Daga Funtua sai Karamar Hukumar Sabuw dake da mutum 232 da suka kamu, sai Kafur mutum215, Charanci 135, Kankara 71 sai kuma Jibiya dake da mutum 69 wadanda suka Kamu.

Haka kuma ko a yawan waɗanda suka rasu, Karamar hukumar Funtuwa ce ke kan gaba wajen yawan waɗanda suka rasu.