DA ƊUMI-ƊUMI: Buhari ya naɗa sabon shugaban Sojoji

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Manjo Janar Faruk Yahya a matsayin sabon shugaban rundinar Sojin ƙasa na Najeriya biyo bayan rasuwar Laftanal Janar Ibrahim Attahiru.

Kafin naɗin nasa, Manjo Janar Faruk Yahaya shi ke jagorantar yaƙi da Boko Haram a Arewa maso gabas.

Ya taɓa riƙe muƙamin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko.