Da Ɗumi-Ɗumi: An miƙa rahoton binciken Abba Kyari ga Babban Sufeton Ƴan Sanda

Babban sufeton ƴan sanda Usman Alkali Baba ya karbi rahoton kwamitin bincike kan tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta Amurka ta yi wa mataimakin kwamishinan ƴan sanda, Abba Kyari.

Tun da farko an dakatar da DCP Kyari a matsayin shugaban rundinar biciken ƙwaƙwafi, biyo bayan tuhumar da aka yi wa ƴan sanda don su binciki lamarin.

Yayin da ake gabatar wa IGP rahoton binciken.

A cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sanda na ƙasa Frank Mba, ya fitar, ya ce Babban Sufeton ya yi alƙawarin yin adalci ga rahoton tare da ɗaukar matakin da ya dace.

  • Da Ɗumi-Ɗumi: An miƙa rahoton binciken Abba Kyari ga Babban Sufeton Ƴan Sanda
  • Ana kashe ƴan Najeriya kamar dabbobi a mulkin Buhari – Gwamna Uzodimma

Sanarwat ta ce, “Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, a yau, 26 ga Agusta, 2021, ya karbi rahoton kwamitin bincike na musamman na da ke binciken tuhumar da FBI ke yi ma tsohon shugaban rundinar (IRT), DCP Abba Kyari. Shugaban kwamitin DIG Joseph Egbunike ne ya gabatar da rahoton, a hedikwatar rundunar da ke Abuja.

“DIG Egbunike, yayin da yake gabatar da rahoton, ya yabawa Babban Sufeton bisa bashi jagoranci binciken tare da membobin kwamitin. Ya kuma ce kwamitin ya fara binciken ne daga lokacin da aka kaddamar da shi a ranar 2 ga Agusta, 2021 kuma ya ce rahoton da aka gabatar sakamakon bincike ne da suka gudanar a tsanake. Ya kuma bayyana cewa rahoton na ƙunshe da kundin zargin, shaidun binciken da kuma bayanan kare kai daga DCP Abba Kyari da sauran mutane da ƙungiyoyi masu alaƙa da lamarin.

“Babban Sufeton Ƴan Sanda, wanda ya yabawa Kwamitin kan aikin da ya gabatar, ya bayyana cewa jigon yin binciken shine a gano gaskiya kan zargin da ake yiwa Jami’in don baiwa rundunar damar zartar da hukunci yanda ya kamata. Babban Sufeton ya ba da tabbacin cewa a natse Kwamitin Gudanarwar Rundunar zai bi shawarwarin da kwamitin binciken ya bayar ya duba sannan kuma tura zuwa wuraren da suka dace don daukar matakai da gaggawa. Ya jaddada jajircewar Rundunar na yi wa kowa adalci”.