Da Ɗumi-Ɗumi: Abduljabbar ya nemi afuwa ga al’umma

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwar al’umar musulumi kan kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu SAW da ake zarginsa da yi, inda ya ce “ba a fahimce ni ba” ne.

Cikin wani saƙon sauti, an ji malamin na cewa “idan har waɗannan kalamai daga ni suke, ƙirƙirarsu na yi, babu su a litattafai to lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni da na gaggauta tuba”.

Ya ƙara da cewa: “Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin waɗancan litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. Sai mu yi roƙon Allah ya haska wa al’umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan ƙarya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su.”

Ana tunanin malamin ya fito ya bayyana haka ne bisa buƙatar yin hakan da ɗalibansa suka nemi ya yi domin a zauna lafiya.