Cikin watanni 12 kacal bayan na zama gwamnan Kaduna, matsalar tsaro zai zamo tarihi a jihar – Isah Ashiru

Dan takardan gwamnan jihar Kaduna a karkashin jami’yyar PDP Isa Ashiru ya bayyana cewa idan za ama gwamnan jihar Kadun, matsalar tsaro zai zamo tarihi a jihar cikin watanni 12 kacal.
Ashiru ya fadi haka ne a zaman da ya yi da kungiyar shugabanin addinin Kirista na yankin Kudancin jihar Kaduna SCKLA a garin Kafanchan ranar Litini.
“Idan har aka zabe ni gwamna rashin tsaro na daga cikin matsalolin da zan fara kakkabewa a cikin shekara daya kacal sannan kuma da sauran abubuwan da al’umman mu suke bukata cikin gaggawa.
“Idan wadanda suke rike da madafun Iko sun yi aiki da gaskiya na yi imani za a iya kawar da rashin tsaro a jihar.
Ya ce ya zama dole a samar da tsaro tare da hada kan mutane saboda jihar ba za ta samu ci gaba ba idan babu zaman lafiya.
Ashiru ya kuma yi wa mutane alƙawarin cewa zai yi adalci wajen yi wa bangarorin jihar ayyukan raya kasa.
Ya ce zai kafa kwamitin domin duba korar ma’aikata da gwamnatin El-Rufai ta yi a baya.
“ Zan kafa kwamitin da za ta gudanar da bincike kan yadda wannan gwamnatin ta kori ma’aikata bisa ka’ida ba.
Shugaban kungiyar SCKLA Emmanuel Kure ya ce SCKLA ta shirya wannan zama ne domin taimakawa kiristoci wajen zabar shugaba na gari a zaben 2023.
“Yin haka zai taimaka wa shugabannin addinin Kirista wajen wayar da kan mutanen su kan zaben shugaba na gari.
Kure ya ce fannin aiyukkan noma, ilimin boko, Samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, inganta masarautun gargajiya, aikin yi, samar da tsaro na daga cikin matsalolin da suke bukatan ‘yan takara su yi wa mutane karin haske akai.