‘Bye Bye Jam’iyyar PDP, na tafi sai wata rana’ – Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar PDP a jihar kuma jigo a siyasar jihar Kano, tsohon gwamna, sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa kwanaki kaɗan suka rage masa a jam’iyyar PDP ya kama gaban sa

Kwankwaso ya shaida wa BBC Hausa cewa saura kafin karshen wannan wata, Maris zai bayyana ficewar sa daga PDP.

Sai dai bai bayyana ko wace jam’iyya zai koma ba.

Sanata Kwankwaso ya kara da cewa rikicin da ke kudundune a PDPn Kano ya sa ba zai iya cigaba da zama a cikinta ba. Ya gwammace ya tattara nasa inasa ya kara gaba can inda zai fi masa da magoya bayan sa.

Idan ba a manta ba, magoya bayan Kwankwado da na gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal sun baiwa hammata iska a wajen zaben mataimakin jam’iyyar PDP na Arewa Maso Yamma, abin bai yiwu ba a Kaduna a wannan ranar zaɓe

Magoya bayansu sun yi ragaraga da akwatinan zaɓe da duka kayayyakin zaɓe a lokacin.

Haka kuma ko a jihar Kano, jam’iyyar a rabe take, ɓangaren Kwankwaso da na Aminu Wali.

Hisham Habib shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Kano ya ce jam’iyyar a shirye ta ke ta yi maraba da duk wanda ya nemi tsunduma cikinta

” Jam’iyyar mu a buɗe take ga kowa da kowa. Duk masu su zo a haɗa kai suzo ayi tafiya tare.

Dama daga PDP ne Kwankwado ya daka tsalle zuwa APC, bayannan sai ya koma PDP, daga nan kuma sai ya koma PDP.

Yanzu dai ana zaton zai koma jam’iyyar NNPN ne.