Buhari ya karrama Minista Sadiya da kyautar inganci da sadaukarwa a aiki

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar da kyautar karramawa ga Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Umar Farouq, saboda gamsuwa da kyautatuwar ayyukan ta na taimako da jinƙan jama’ar Nijeriya.
Shugaban ya ba da kyautar mai suna Karramawa kan Kyautatuwar Aikin Jama’a ta Nijeriya (Nigeria Excellence Award in Public Service, NEAPS) ga ministar da kuma wasu mutum 44 a ranar Juma’a a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
A bikin, Buhari ya bayyana cewa an ba da kyaututtukan karramawar ne bisa la’akari da mutanen da su ka yi zarra kuma su ka zama misali wajen wa al’umma aiki bilhaƙƙi da gaskiya.
Ya faɗa wa waɗanda aka karrama ɗin cewa: “An samar da wannan kyautar karramawar ne bisa sahihiyar hujjar nasarorin da ku ka samu a sassa daban-daban na tattalin arzikin ƙasar nan.
“Za a ba ku wannan karramawa ne saboda kun yi zarra wajen yi wa al’umma aiki kuma ku ka ba da gudunmawa ga kawo canji mai ma’ana a ƙasar nan.
“Wannan abin koyi ne ga shugabannin yanzu da masu zuwa nan gaba domin su ƙara himma wajen aikin ciyar da ƙasar nan gaba.”
A jawabin da ta yi bayan an yi mata wannan karramawa, Minista Sadiya ta bayyana jin daɗi da aka zaɓe ta aka ba ta wannan kyauta ta NEAPS.
Ta ce: “Wannan wani muhimmin zango ne, musamman a rayuwa ta, domin wannan karramawa shaida ce ƙarara ta gamsuwar da aka yi da ‘yan nasarorin da na samu a wajen ayyukan da na yi wa jama’a ya zuwa yanzu da kuma alhakin da aka ɗora mani a fagen ayyukan inganta rayuwa da jinƙai a cikin ‘yan shekarun nan.
“Ina so in ƙara miƙa matuƙar godiya ga mai girma Shugaban Ƙasa saboda damar da ya ba ni na yi wa ƙasa ta aiki a matsayin Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, sannan ta hanyar wannan muƙamin na yi ƙoƙarin bautata wa ɗimbin mutane marasa galihu waɗanda ke cikin buƙatar a inganta rayuwar su da taimakon jinƙai cikin gaggawa a faɗin ƙasar nan.
“Haka kuma ina godiya matuƙar gaske ga kamfanin ‘TBS Media’ da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya da su ka ga dacewa ta har su ka ba ni wannan babbar kyauta ta NEAPS ta shekarar 2022 a ɓangaren ayyukan jinƙai, kuma su ka ɗora ni kan matakin shiga da’irar sauran manyan ‘yan Nijeriya waɗanda su ma aka karrama su tare da ni a yau.”
Ministar ta sha alwashin za ta ci gaba da yin bakin ƙoƙarin ta wajen yi wa ƙasar nan aiki wanda yin shi ne gudunmawar ta wajen taimakawa a tsamo Nijeriya daga cikin matsalolin da su ka addabe ta.
Mai taimaka wa ministar a fagen aikin jarida, Nneka Ikem Anibeze, ta yi ƙarin bayanin cewa wannan kyautar karramawa da aka yi saboda aiki ga jama’ar Nijeriya “manufar ta ita ce a karrama muhimman ayyukan da aka yi wa jama’a a Nijeriya ta hanyar gudunmawar da jama’a ɗaiɗaiku da jihohi da mutanen unguwa su ka bayar wajen shugabanci da aikin jama’a da jinƙai.”
Waɗanda su ka shirya bikin karramawar dai su ne Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) da wani kamfani mai suna ‘The Best Strategic Media’ (TBS).