Buhari ya baiwa Babagana Kingibe sabon muƙami, ya cire shugaban hukumar NEMA

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Ambasada Babagana Kingibe a matsayin jakadan Najeriya na musamman a ƙasar Chadi da yankin Tafkin Chadi.

Wannan sanarwa na ƙunahe ne cikin wata tarda da Kakakin fadar shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya fitar a yammacin Litinin.

Haka zalika shugaban ƙasan ya cire shugaban hukumar bada agajin gaggawa na ƙasa (NEMA) AVM M. A Muhammad tare da maye gurbbinsa da Ahmad Mustapha Habib.

A halin yanzu, AVM M. A Muhammad shine shugaban sabuwar hukumar kula da dattawa ƴan sama da shekaru saba’in da aka ƙirƙiro.