Buhari bai zo Sokoto ya yi ta’aziyyar yadda ake yi wa mutane kisan gilla ba , amma ya garzaya Legas bukin kaddamar da littafin Akande – Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya nuna rashin jin daɗin sa kan yadda a cewarsa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da mutanen yakin ana ta kashe su amma babu wani abu da gwamnatin ke yi wajen kawo karshen bala’in.

Bafarawa ya bayyana takaicinsa kan yadda shugaba Buhari yayi tattaki har Legas domin halartar bukin ƙaddamar da littafin tarihin (Bisi Akande) amma ya gagara zuwa Sokoto ya yi wa mutane ta’aziyyar rayukan da ake yi wa kisan kiyashi.

Buhari ya bi mutane gida-gida a lokacin da yake neman kuri’a, wato lokacin yana buƙatar su, amma yanzu da yake ya samu abinda ya ke so bai iya zuwa ya ga talakawan da suka zabe sa ba yayi musu jaje da ta’aziyyar rayukan su da ake kashewa kamar kiyashi ba.

Idan ka ga Buhari ya fita sai dai idan zai tafi neman lafiyar sa, shi ya san daɗin lafiyar sa da neman magani amma bai san darajar rayukan mutanen da suka zaɓe shi ba.

Bafarawa ya kara da cewa sun yi kokarin su samu ganin shugaba Buhari domin su sanar da shi tsananin abinda ke faruwa amma hakan bai yiwu ba.

” A baya ai shi ya ke neman mutane gida-gida. Ya zo gidan nan ya biɗi mutane amma yanzu fa. Ba ta talakawa ya ke ba.

Buhari ya sani zai gamu da Allah kuma domin a ƙarkashin sa ne ya ake rasa rayukan waɗanda basu ji ba ba su gani ba.

Idan ba a manta ba shugaba Buhari ya sa ciki baki da yin kurin cewa ko wata biyu ba za ayi ba idan ya ɗarr kujerar mulki zai kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, tun a lokacin da ma Boko Haram ne ke gallaza wa mutane azaba a kasar.

Sai ga shi yanzu a ƙarƙashin ikon sa matsalar rashin tsaro a Najeriya ya nunka na lokacin Jonathan yadda ko kwatantawa ba a iya yi.