Buhari bai taɓa shaida wa kowa cewa za a cire tallafin mai ba – Sanata Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa a yanzu dai ba za a cire talalfin man fetur ba, kamar yadda jaridu da soshiyal midiya su ka riƙa yayatawa.

Lawal ya bayyana haka a ranar Talata da dare, ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ganawa a keɓance da Shugaba Muhammadu Buhari.

Kamar yadda Lawan ya bayyana masu, ya ce Buhari ya ce masa bai sanar da kowa cewa zai cire tallafin mai kamar yadda aka riƙa yayatawa ba.

“Na tattauna da Shugaban Ƙasa kan batutuwa da dama, ciki har da batun masu tayar da ƙayar baya a wasu sassan ƙasar nan.

“Jama’a da dama na nuna damuwar su kan batun cire tallafin fetur. To a matsayin mu na wakilan jama’a, dole mu ma wannan batu ke damun mu.

“Na samu Shugaban Ƙasa kuma ya sanar da ni cewa bai sanar da kowa cewa zai cire tallafin fetur ba.”

Cikin watan Nuwamba Premium Times Hausa ta yi sharhin batun biyan ‘yan Najeriya miliyan 40 alawus ɗin Naira 5,00 idan an cire tallafi mai, har ta yi tambayar shin ‘Shafa Labari Shuni’ Ko ‘Hikayoyin Shehu Jaha’?

An shafe shekaru gwamnatin Najeriya ta kan zirin siraɗin ƙoƙarin cire tallafin man fetur. A duk lokacin da aka yi ƙoƙarin cirewa, ‘yan Najeriya kan fusata. Sai dai a wannan karon, Gwamnatin Buhari za ta cire ɗin, domin har ma ta saka batun cire tallafin a cikin kasafin 2022.

Gwamnatin Tarayya na ganin cewa tallafin fetur na taimakawa ga talakawa, domin idan fetur ya yi tsada, su ne ke fin shan wahalar ƙuncin rayuwa.

Sai dai duk da wannan, cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe na duniya, irin su IMF, su a ganin su, tallafin fetur na hana ƙasar nan ci gaba tare da kasa samar wa ‘yan ƙasa ayyukan inganta rayuwa da ci gaba.

Tsakanin 2006 zuwa 2018, Najeriya ta kashe naira tiriliyan 10 wajen biyan kuɗin tallafin mai. Wani bincike da gwamnatin Birtaniya ta gudanar, ya nuna cewa kuɗin da Najeriya ta kashe kan tallafin mai a wadancan shekarun, sun zarce kasafin kuɗin Najeriya na fannin ilmi da na fannin tsaro baki ɗaya daga 2006 zuwa 2018.

Hukumar NNPC ta ce a cikin watanni takwas su ka gabata, ta kashe naira biliyan 816 wajen cike gurbin tallafin fetur.

An Ki Cin Biri An Ci Kare: Za A Daina Biyan Tallafi Ko Koma Biyan Wani Sabon Tallafi:

Sabuwar Dokar Fetur ta 2021 ta haramta biyan tallafin fetur daga tsakiyar 2022, kamar yadda IMF ya bada shawara.

Amma kuma Gwamnatin Tarayya ta ce za ta riƙa biyan talakawa miliyan 40 naira 5,000 kowane wata, matsayin kuɗin rage masu raɗadin tsadar kuɗin shiga motar haya da babu makawa sai ya nunka, idan aka ƙara wa fetur kuɗi.