BUA ya rabawa ma’ikatansa kyauta na biliyoyin naira a matsayin tukuici

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Isyaka Rabiu kuma babban mai hannun jari mafi girma a kamfanin Simintin BUA ya rabawa ma’ikatansa kyautan wani kaso cikin hannun jarinsa a kamfanin.

Kason, wanda ya kusan naira biliyan biyu, ya yi hakan ne a matsayin tukuici ga ƙoƙarin da ma’aikatan suka yi na aiki tuƙuru da ya kai kamfanin ga samun gwagwaban riba da bai taba samu ba duk da halin tsaka mai wuya da annobar Korona ta sanya fannin kasuwanci.

A cewar ofishin shugaban kamfanin, Abdul Samad Rabiu ya ce yi haka ne a matsayin yabo ga ƙoƙarin manyan ma’aikatan kamfanin waɗanda suka taka rawar gani wurin samun wannan nasara duk da bullar annobar Korona a 2020.

Duk da halin ƙaƙani kayi da bullar cutar korona ta jefa tattalun arziƙi a ciki, kamfanin Simintin BUA ya sanar da samun ƙaruwar kashi 19.3 na riba da naira biliyan N209.4 a shekarar 2020, wanda a shekarar 2019 naira biliyan N175.5 ne ribar da kamfanin ya samu.

Jaridar Daily Nigeria ta ruwaito Kamfanin ya bayyana cewa, naira biliyan N209.4billion riba ce zalla bayan Harajin naira biliyan N72.3 da kamfanin ya biya gwamnati.