Boko Haram da ƴan bindiga sun lahanta sojoji 7,403 -Shugaban Asibitin Sojoji

Aƙalla sojoji 7,403 ne su ka samu nakasa raunuka, lahani ko nakasar da ta kassara jiki, wadda waɗansu har abada za su ƙare rayuwar su cikin nakasa.

Shugaban Riko na Asibitin Kwantar da Sojoji na Jihar Kaduna (44 Army Reference Hisoital, Kaduna) ne ya bayyana wa tawagar Majalisar Dattawa haka, a lokacin da su ka kai ziyarar gani-da-ido asibitin da ke Kaduna, a ranar Asabar.

Shugaban, Stephen Omochukwu ya bayyana cewa sojojin masu ɗimbin yawa haka sun ji munanan ciwo ne wurin gumurzun yaƙi da Boko Haram ko ‘yan bindiga.

“Wasu an duba su, an kula da su kuma an ba su magunguna sun warke, an sallame su. Wasu kuma an sallame su da nakasa a jikin su, wasu kuma an lahanta su, lahanin da har abada ba za su iya komawa daidai ba. Su na ma buƙatar kayan aikin da sai da su za su iya rayuwa.

“Kalubalen da mu ke fuskanta mu ma’aikata da majiyyata ke fuskanta kenan a wannan asibiti mai cin gadaje 600.

“Mun karɓi sojoji 7,403 tun daga farkon fara yaƙin Boko Haram a wannan asibitin.

“Wasu har abada ba za su warke ba. Kamar irin waɗanda aka guntule wa hannaye, wasu ƙafafu aka datse masu. Da yawa sun samu cutuka ne a daji wajen yaƙi da ‘yan ta’adda. Wasu kuma abin ya taɓa masu ƙwaƙwalwa. Kuma da dama waɗanda ke fama da damuwa.” Inji shi.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Karanta bayyana cewa Majalisa za ta ƙara ƙaimi wajen ganin ana yi wa sojoji dukkan abin da ya dace da wanda ya wajaba a riƙa yi masu.