BINCIKE: Yadda Shirin Dashen Miliyoyin Itatuwa ya tashi a tutar iska, bayan gwamnati ta yi asarar naira miliyan 30

Ƙoƙarin Gwamnantin na dasa miliyoyin itatuwa domin magance canjin yanayin gurgusowar hamada ya samu tawaya, bayan an kashe wa shirin naira miliyan 30.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da shiriricewar shirin a ƙasa da cewa uku bayan kammala shi.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kashe naira miliyan 30.4 wajen gagarimin shirin dashen itatuwan da ta fara ƙaddamarwa a Jihar Oyo.

To amma kuma yayin da PREMIUM TIMES ta kai ziyara, ta samu itatuwan da aka dasa ‘yan ɗaruruwa ne, maimakon miliyan shida da aka ce za a dasa.

“Mun Dasa Itatuwa Da Yawa, Amma Sun Mace” -Jami’an Gwamnati

Jami’an kula da dashen itatuwan sun bayyana wa wakilin mu cewa an dasa Itatuwa masu yawan gaske, amma rashin ruwa a kashe su.

Amma kuma abin da PREMIUM TIMES ta bankaɗo ya tayar da hankulan masu rajin kare yanayi da masana illar zaizayar ƙasa, har su ke tababar yadda aka aiwatar da shirin dashen itatuwan.

Wani Babban Masanin Zaizayar Kasa mai suna Enoabasi Anwana da ke Jami’ar Uyo, ya ce, “Ziyarar da aka kai wuraren da ya kamata a yi dashen itatuwan ta nuna cewa an yi ƙwange da algusshu wajen dashen itatuwan.”

Cikin 2017 da 2019 Najeriya ta nemi bashin naira biliyan 10.69 da kuma Naira biliyan 15 domin yaƙi da matsalar yanayi da zaizayar ƙasa da kuma samar da korayen bishiyoyi a wuraren da ke da matsalar yanayi.

Daga cikin wuraren da ake so a dawo da martabar yalwar Itatuwa da ke bayar da inuwa, har da dandalin shaƙatawa na Jihar Oyo.

A ƙarƙashin wannan shirin ne aka ce an kashe Naira miliyan 30.04. An fara shirin a ƙarƙashin Ma’aikatar Kula da Raya Muhalli ta Ƙasa, cikin 2019.

Yayin ziyarar, PREMIUM TIMES tare da wasu masana yanyin muhalli su biyu sun lura da cewa akwai matsala a ayyukan da aka ce an gudanar a cikin al’ummar Igbeti, Alaguntan da Tede, waɗanda ke maƙwautaka da dandalin shaƙatawa na Oyo.

Mataimakiyar Daraktar Gandun Shaƙatawa, R.I Muraina ya ce an dasa itatuwa miliyan shida a fili mai faɗin kadada 15 a yankunan uku.

Wani allon sambodi da wakilin mu ya gani, ya na ɗauke da rubutun cewa an shuka katako, kashu, mangwaro da lemon zaƙi a Igbeti da Alaguntan.

Yayin da Muraina ya yi iƙirarin an dasa ko an shuka Itatuwa miliyan shida, binciken wannan jarida ya gano ba su wuce ‘yan ɗaruruwa ba.

Wani ƙarin abin mamaki ma shi ne wakilin mu ya iske ana noman rogo, waken soya, masara da dawa a wurin.

Wani mai kula da Dandalin Shaƙatawa ya ce mazauna yankin sun shuka amfanin gona ne a wurin domin gudun kada ciyawa ta fito ta haɗiye wurin.