BARKWANCI: Sauron da aka yi wa allura da maganin kara karfi maza basu fice daga dakin gwaje-gwaje na Wuhan ba – Binciken DUBAWA

Zargi: Wani sakon da ake yadawa a WhatsApp na zargin cewa akwai wasu dubban Sauron da aka yi wa allura da maganin karawa maza karfi (Viagra) da suka kubuce daga wani dakin gwaje-gwaje a China, bayan an yi amfani da tsauraran matakan tsaro wajen kulle su.

Wani sakon da ya danganci COVID-19, wanda ke yawo a WhatsApp a kasar Saliyo na zargin cewa akwai dubban sauron da aka alkintawa kwayoyin halittarsu aka kuma yi musu allura da Viagra- wato maganin da ke karawa maza karfi wadanda suka kubuce daga wani dakin gwaje-gwaje. Dama dai an yi amfani da matakan tsaro masu tsauri wajen kulle wannan dakin gwaje-gwaje a China kuma ana zargin cewa duk namijin da sauron ya ciza zai rika sha’awa…

Ga abun da aka bude sakon da shi:

“illar da cizon sauro kwaya daya zata yi a jikin mutun zai kai tsawon sa’o’i 40 kafin ya warware. A cewar Dr Wengi Ying Yin Jing.

Tantancewa

Wannan labarin ya yi mafari ne a shafin jaridar World Daily Report. Mun gano cewa wannan shafin na barkwanci ne. A karkashin tambarin wannan shafin, akwai inda suka ce “gaskiya ba ta da mahimmanci a nan.” Bugu da kari, shafin da ke dauke da takaitaccen bayani kan abubuwan da suke wallafawa (About Us) sun bayyana haka:

“WNDR ta dauki nauyin yanayin barkwancin labaranta da ma abubuwa marasa gaskiya da ke cikin labaran. Duk mutanen da muka yi amfani da su a cikin labaran, – hatta wadanda aka yi amfani da abubuwan da suka faru a zahiri – ba gaskiya ba ne. haka nan kuma, idan akwai wanda ya yi kama da wanda kuka gani a cikin labarabmu ko yana raye ko ya riga mu gidan gaskiya ko kuma ma ya dawo daga matattu, almara ce”

To sai dai gabatarwar labarin, bai bayyana cewa labarin barkwanci ne ba kawai, dan haka yana yaudarar jama’a masu karantawa.

Bayan haka, hoton wani wanda aka kwatanta a matsayin mai shekaru 87 na haihuwa a labarin inda ake zargin cewa an kwantar da dattijon a asibiti sakamakon cizon irin sauron karya ne. Ainihin mutumin da ke hoton, wani tsoho ne dan Japam wanda ya kai shekaru 114 na haihuwa kafin ya rasu ranar 28 ga watan Satumbar 2003. Dattijon mai suna Yukicji Chuganji ya dade da mutuwa kafin wannan zargin ya bulla a shafinsu a matsayin masu fama da radadin cizon Sauron.