Barazanar ƴan bindiga ne ya sa na cire yarona daga makarantar gwamnati- El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa ya cire ɗansa Sadiq daga makarantar gwamnati da ya saka shi.

Jaridar Daily Trust ce ta fara ruwaito yadda gwamnan ya cire ɗan nasa mai shekara shida daga makarantar Kaduna Capital wanda ya saka shi a 2019.

Cikin wata hira da kafar BBC Pidgin, El-Rufai ya ce ya cire shi ne saboda yadda ‘yan fashin daji ke ƙoƙarin kai wa makarantar hari domin sace yaron nasa, musamman saboda a kare rayuwar sauran yara.

Ya ƙara da cewa ya saka ‘yarsa ma mai suna Nasrin a makarantar lokacin da ta cika shekara shida da haihuwa.

“Mun cire su ne na ɗan wani lokaci saboda tsaron makarantar, saboda mun daƙile harin ‘yan fashi har sau biyu a kan makarantar da ke yunƙurin sace ɗana.

“Ba na tunanin za su samu nasara saboda akwai cikakkun jami’an tsaro a wurin amma za a saka rayuwar sauran yaran cikin haɗari…suna so su ga idan suka sace ɗan nawa zan biya kuɗin fansa ko ba zan biya ba.”

Gwamnan ya ce yanzu haka yaran suna gida, inda ake yi musu darasi amma za su rubuta jarrabawa a makarantar.