BANKWANA DA 2021: Masu Gudu Su Gudu: Ashe talakawa ne za su gudu, ba ɓarayin gwamnati ba

Kada ka daɗa ka kada ka rage, babban dalilin da ya sa talakan Arewa ya zaɓi Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 har ma a zaɓukan shekarun baya da bai yi nasara ba, shi ne domin a tunanin talaka, Buhari ne kawai zai iya ɗaure manyan ɓarayin gwamnati. Wannan dalili shi ne ‘farilla’, duk sauran dalilai kuwa daga ‘sunna’ sai ‘mustahabbi.’

Shi ya sa a cikin makon da aka bayyana nasarar Buhari a kan Jonathan, sai mawaƙin APC kuma mawaƙin Buhari, wato Dauda Kahutu Rarara ya fito da waƙar “Masu Gudu Su Gudu.”

Daga 2015 zuwa yau makon ƙarshe na 2021, har yau banda tsohuwar Ministar Fetur, Diezani Allison-Madueke, ita da tsohon Ministan Shari’a, Mohammed Adoke, babu wani gazagurun ɓarawon gwamnati da ya tsere gudun hijira.

Adoke ya dawo tuni, an kama shi kuma tuni aka sake shi da sunan beli.

Har yau babu tsoffin gwamnoni uku gangariya ko tantagaryar ministoci uku gangariya, waɗanda ke ɗaure bayan hawan mulkin Buhari tun daga 2015 zuwa zuwa Disamba, 2021.

Ashe talakawan ne za su gudu, kuma su ne za a riƙa tssrewa. Allah kaɗai ya san yawan talakawan Arewa da su ka tsallake gidajen su a guje, su ka yi gudun hijira. Kuma Allah ne kaɗai ya san yawan talakawan da ke tsare a cikin rayuwar ƙunci a hannun ‘yan bindiga. Haka nan kuma Allah ne kaɗai ya san yawan talakawan da aka tsare, sannan aka biya kuɗin fansar su kafin a sake su.

Katsinawa sun gudu, Zamfarawa sun gudu. Sakkwatawa sun gudu, Zazzagawa sun gudu. Bafulatani ya gudu, Bakabe ya gudu. Bahaushe ya gudu, Banufe ya gudu. Miji ya gudu, mata ta gudu. Tsoffi sun gudu, yara sun gudu. Malam ya gudu, basarake ya gudu. Attajiri ya gudu, talaka ya gudu. Shi kuma ɗan PDP da ya gudu, sai ya yi tasa hijirar a cikin APC, ya yi bakam abin sa.

Masu Gudu Su Gudu: Yadda Talakawan Katsina Su Ka Yi Wa Mulkin Buhari Gudun Da Ba Su Yi Wa Mulkin Jonathan Ba

Bayanin da PREMIUM TIMES Hausa za ta yi a kan talakawan Katsina, ya isa babban misali kan irin gudun da talakawan Sokoto, Zamfara da Neja da Kaduna su ka yi. Saboda wannan jarida ba ta buƙatar buga misalin abin da ke faruwa a jihohin. Labarin halin da Katsinawa ke ciki, ya wadatar.

A Jihar Katsina ɗin ma PREMIUM TIMES Hausa za ta yi bayani ne a ƙaramar hukuma ɗaya tal, wato Faskari. A cikin Faskari ɗin ma, bari mu ɗauki yankin Dagaci/Maigarin Ruwan Godiya kaɗai.

Masu Gudun Katsina: ‘Ƙauyukan Da ‘Yan Bindiga Su Ka Kori Talakawa A Ruwan Godiya, Yankin Faskari’ -Hira Da Ɗaan Gudun Hijira:

“Mu na jin ana cewa ‘yaƙi mai tada gidan gona’, to a yau dai wannan abu ya zo kan mu. Domin ka gan ni nan, a zaman gudun hijira na ke yi, ni da iyali na mu 20. Mun bar cikin ƙauyen mu da ke yankin Ruwan Godiya a Karamar Hukumar Faskari.

“Garuruwan da ‘yan bindiga su ka fatattaki mutane kowa ya gudu ba kowa a garin, sun kai 100 a Faskari kaɗai. Wasu sun gudu zuwa cikin Faskari, wasu sun yi Kano, wasu Funtua, wasu Malumfashi, wasu a cikin Sheme, wasu Kakumi ko sauran garuruwan kusa, waɗanda ‘yan bindiga ba su kai kan su ba.

“A mazaɓar Ruwan Godiya, babu kowa a garin Unguwar Hajiya. Ba kowa Unguwar Nadada. Mutanen Kanawa, Kutaru, Unguwar Goga, ‘Yantuwaru, Shawo da Kifai duk babu kowa. Wasu garuruwan ma ‘yan bindiga ke kwanciya a ciki su na hutawa.

“An kori kowa a Kuka Shida. Mutanen Kuka Uku sun tsere, ba kowa. Garin Mununu kowa ya fashe, tun ranar da aka kwashi mutum 108 a garin. Kuma yau kwanan su 25 kenan a hannun ‘yan bindiga, ko labarin su ba a yi a kafafen yaɗa labarai ba. Kuwa akwai ‘yan uwan mu na jini da aka kama a cikin su. Yanzu haka mata masu ciki da aka kama a Mununu akwai wadda ta haihu a hannun ‘yan bindiga.

“Ni na ke faɗa maka. Babu kowa a Remanya da Bakarya da ƙauyen Mashi da Zarin Kwari da Zarin Tudu. Babu kowa a ‘Yar Santa da Liggel da Kaye. Dukkan mu ɗin nan da ka ke gani a nan, tun cikin damina mu ke gudun hijira.”

Masu Gudun Katsina: ‘Mabugi Kusa, Maceci Nesa’ -Ɗan Gudun Hijira

“Babu abin takaici kamar yadda ga sojoji kusa da mu, amma ba su iya magance mana komai. Su ke kusa da mu, ‘yan bindiga na can nesa da mu. Amma abin sai ya koma su ‘yan bindigar sun fi kusa da mu, su kuma sojojin ke kesa da mu.

“Abin ya zame mana mabugi kusa, maceci nesa. To ga soja a Sheme, bai magance farmaki a Kwakware. Ga soja a Ruwan Godiya, bai magani a Kwai.”

PREMIUM TIMES Hausa ta ɓoye sunan wanda ta tattauna da shi, saboda dalilan tsaro.