Bankin Duniya ya dakatar da tallafin ƙasar Uganda, saboda haramta wa namiji ya nemi namiji

A ranar Talata ce Bankin Duniya ya bada sanarwar dakatar da tallafin kuɗaɗe ga ƙasar Uganda, saboda ƙasar ta kafa dokar haramta namiji ya nemi namiji ko namiji ya auri namiji a ƙasar.
Cikin wata sanarwar da Bankin Duniya ya fitar a ranar Talata, ya ce dokar hana namiji ya nemi namiji a Uganda ta saɓa wa ɗabi’ar Bankin Duniya a tafarkin daƙile fatara da talauci a duniya, ba tare da nuna bambanci ga kowane ɗan Adam ba.
Hukuncin da Bankin Duniya ya ɗauka ya biyo ne bayan da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin jama’a da Majalisar Amurka sun takura wa bankin cewa ta dakatar da tallafin da ta ke bai wa Uganda.
A ranar 29 Ga Mayu ce Shugaba Yoweri Museveni ya sa wa Dokar Haramta Luwaɗi hannu a Uganda. Hukuncin wanda aka kama namiji ya nemi namiji ko ya auri namiji kuwa, ya haɗa har da hukuncin kisa.
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Human Right Watch, ta ce dokar hana namiji ya nemi namiji a Uganda ta tauye haƙƙin ɗan Adam.
A cikin watan Mayu ne dai shi ma Shugaban Amurka Joe Biden ya ce “dokar hana namiji ya nemi namiji a Uganda ta tauye ‘yancin ɗan Adam, kuma ba ta dace da al’ummar Uganda ba. Kuma za ta kawo naƙasu ga tattalin arzikin ƙasar.”
Biden ya yi barazanar ƙaƙaba wa Uganda takunkumi, su kuma ‘yan majalisar Amurka masu kare LGBTQ+ a duniya su ka ƙara zuguguta cewa lallai Bankin Duniya ya dakatar da tallafin da zai bai wa Uganda.
LGBTQ+ dai ta ƙunshi ‘yan maɗigo, luwaɗi, mata-maza, namijin da ya koma mace (Bobriskanci) da makamantan su.
Sama da ƙungiyoyi 170 a duniya su ka soki ƙasar Uganda da don ta kafa dokar haramta namiji ya nemi namiji.
“Mu muradin mu shi ne mu kare mutane marasa rinjaye da al’umma ta tsane su, saboda jinsin su.” Cewar Bankin Duniya.