Ba ƙulunbutun ‘Kayan matan’ Jaruma bane ya yi sanadiyar rabuwa ta da Laila Charani – Inji attajiri Ned Nwoko

Babban lauya kuma attajiri, Ned Nwoko ya yi karin haske kan dalilin rabuwarsa da matarsa da ya aura daga kasar Morocco Laila Charani.

A ranar 1 ga Nuwamba Laila matar Nwoko na biyar ta sanar da mutuwar auren ta a shafinta na Instagram.

Wannan sanarwa ya sa mabiyansu yin korafin cewa ‘Kayanmata’ da Hauwa Mohammed wacce aka fi sani da Jaruma ke siyarwa ne yayi sanadiyyar mutuwar auren.

Nwoko wanda ya auri Jaruma ‘yar fina-finan Nollywood Regina Daniels a watan Afrilu 2019 ya yi magana bayan wata daya da rabuwa da Laila inda ya ce ya rabu da matarsa saboda wasu dabi’u da take yi da bai yi kama da na matar aure ko na Uwa ba.

Ya ce ya lula da wannan muguwar dabi’a na matar sa a lokacin da ta je hutu Landan da ‘ya’yan su uku.

Nwoko wanda ya sanar da haka daga bakin masu taimaka masa kan harkokin yada labarai ya ce ya gano cewa matar sa na tare da wani saurayinta da ta hadu da shi tun a watan Janairu.

“A dalilin tarayyarta da wannan saurayi Laila ta daina kula yatan mu sannan duk kuɗaɗen da na aika mata domin walwalan ‘ya’ya na ta kashe a kanta da saurayinta.

Nwoko ya kuma ce ya gano cewa Laila ta je ta yi fiɗan gyaran jiki da ake yi na zamani ba tare da izininsa ba yayin da take hutu a Landan.

“Garin yawon da take yi da saurayinta Laila ta kamu da cutar korona a wani kulob sannan har ‘yan sanda sun kamata a Landan.

Ita dai Laila ta ce shairi kawai aka yi mata. Sannan bata fadi dalili ko wanda ya yi mata shairi ba.

Ned Nwoko suna ne da ya fara tashe ya karaɗe shafukan yanar gizo bayan da ya auri Regina Daniels a matsayin matarsa ta bakwai.