An yi zaman sulhu tsakanin Kabiru Gombe da Muazu Magaji

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Shugaban Matasan Ɗariƙar Tijjaniyya Sheikh Ahmadu Tijjani Umar ya shirya zaman sulhu tsakanin Engr. Muazu Magaji, tsohon Kwamishinan jihar Kano da Sheikh Kabiru Gombe a gidan Sheikh Bala Lau na Babbam Birnin Tarayya Abuja.

Engr. Muazu Magaji ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a yammacin Asabar.

  • Sunsa Shugaban Matasan Darikar Tijjaniya Sheik Ahmadu Tijjani Umar a yau ya hada zama na sulhu da bada hakuri ga Sheik Kabiru Gombe a gidan sheik Bala Lau da ke Babban birnin Tarayya Abuja….tare danuwa kuma abokinmu Garba Deen Muhammed GGM NNPC.

    Allah ya saka da Alkhairi…Ya Allah ka yiwa Sheik Ahmadu Tijjani Gwabnan Kaduna , mu kuma ka bamu Kano don ci gaban Alummah, addinin mu da arewacin Nigeria”.

    Sheikh Kabir Gombe da Engr. Muazu Magaji

    A jiya Juma’a ne Malam Kabiru Gombe ya yi barazanar kai Muazu Magaji kotu har in bai janye wata magana da Malamin ya ƙira da ‘ƙage’ inda ɗan siyasan ya wallafa wani rubutu da ya kwafo daga wani shafin bogi dake cewa su Kabiru Gombe sun ce za su fice daga APC muddin Mai Mala Buni ya dawo da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma APC. Kabiru Gombe ya ce ƙarya ne rubutun domin ba su san da shi ba.