AN YANKA TA TASHI: Kotu ta soke korar-kare da Hukumar Sojojin Najeriya ta yi wa wani Janar

Kotun Sauraren Ƙararraki a Abuja ta umarci Hukumar Sojojin Najeriya ta maida Burgediya Janar A.S.H Sa’ad kan muƙamin sa na soja, bayan korar sa da aka yi cikin 2016.

Ann dai kori Sa’ad tun cikin 2016, tare da wasu sojoji 37.

Yayin da Mai Shari’a Benedict Kanyip ke yanke hukunci, ya ce wanda aka korar ya gamsar da kotu 100 bisa 100 cewa korar da aka yi masa ba bisa ƙa’ida aka yi ta ba.

Dama can a baya wannan jarida ta buga labarin yadda aka tilasta wa manyan hafsoshin sojojin su 38 barin aiki tun lokacin su bai yi ba, kuma ba da son ran su ba.

Akasarin waɗanda aka korar dai ba a taɓa kama ko ɗayan su da wani laifi ba, ballantana a ba shi takardar gargaɗi. Dalili kenan a lokacin aka riƙa suka da caccakar Hukumar Sojojin Najeriya cewa ta yi ƙarfa-ƙarfa da kuma bi-ta-da-ƙulli, dukan kabarin kishiya.

Ganin haka, sai waɗanda aka korar su ka rubuta takardar kuka ga Shugaba Muhammadu Buhari, kamar yadda doka ta tanadar, domin a bi masu ƙaƙƙin su.

Sai dai kuma kukan da su ka aika wa Buhari ya zama ihun-ka-banza, domin zai da aka shafe shekaru biyu ba a bi ba’asin komai ba.

Ganin yadda Buhari ya watsar da lamarin su tsawon shekaru biyu, sai aka riƙa zargin Buhari cewa da hannun sa da sanin sa aka kori sojojin, ba tare da sun aikata laifin komai ba.

Amma yayin da Mai Shari’a Kanyip ke yanke hukunci, ya ce wanda ya shigar da kara ba za a kore shi ko a tilasta masa yin ritaya ba, domin ba a same,shi da laifin komai ba.

Kanyip ya ce ba zai iya ƙara wa mai shigar da ƙarar wa’adin da ya zarce 2019 ba, shekarar da ya kamata ya cika shekaru 35 a aikin soja, inda ya kamata ya yi ritaya.

Sannan kuma kotu ba ta roƙi a ƙara masa muƙami zuwa Manjo Janar, kamar yadda aka ƙara wa tsarar sa a aikin, waɗanda su ka yi ritaya cikin 2019.

“Hukumar Sojojin Najeriya ta gaggauta biyan sa albashin sa na tun daga ranar da aka kore shi, har zuwa ranar lokacin yin ritayar sa cikin 2019.” Inji Mai Shari’a Kanyip.