An kama waɗanda suka yi garkuwa da yaran makarantar Tegina

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sakkwato, Kamaldeen Kola Okunkola ya gabatar da bata-gqri da ƴan ta’adda da jamu’an sa suka yi nasarar kamawa a ƴan kwana-kwanan nan a ci gaba da yaƙi da suke yi da miyagun iri a faɗin jihar.

Ya bayyana haka ne a wata sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar jihar, ASP Sanusi Abubakar wanda ya rabawa manema labarai a ranar Talata a Sakkwato.

Sanarwar ta ce daga cikin waɗanda hukumar ta kama har da wani daga cikin waɗanda suka sace ɗaliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko na Tegina.

  • Facebook

    Twitter

Labarin bayaBuhari ya kori shugaban hukumar NAPTIP

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce dake da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jaridu.