An fara muƙabalar Abdul-Jabbar da Malaman Kano, Farfesa Salisu Shehu ne Alƙali

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

A halin yanzu an fara gudanar da Muƙabala da gwamnatin jihar Kano ta shirya tsakanin Malam Abdul-Jabbar Nasiru Kabara da Malaman Kano.

BBC Hausa ta ruwaito Malaman da za su yi Muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara su ne; Malam Abubakar Mai Madattai daga bangaren Tijjaniyya da Malam Kabir Bashir Kofar Wambai bangaren JIBWIS, wato Izala da kuma Dr Rabi’u Umar Sani Rijiyar Lemo daga bangaren Salafiyya, sai kuma Malam Mas’ud Hotoro daga bangaren Kadiriyya.

Shugaban jami’ar Al-Istiqama Sumaila, Farfesa Salisu Shehu, ne Alkalin mukabalar. Legit Hausa ta ruwito.