An fa kai ni makura yanzu, wadanda ke ganin ba a isa a kan su ba, su saurare ni – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadi da kakkausar murya cewa lallai fa yanzu an lai shi makura, duk wanda yake ganin ya isa, yana abinda ya ga dama a kasar nan, zai yaba wa aya zaki.

“Wasu yan tsiraru suna ganin ba a isa akan su ba toh za su gwamnace kidi da karatu domin gwamnati daga yanzu ba za ta sake daga wane mutum kafa yana abinda ya ga dama ba.

” Wadanda ke abinda suka dama a wani yankin kasar nan, ba su san abinda ya faru ba a lokacin yakin basasa, mu da muka yakin na wata 30, mun san abinda muka gani, amma zamu nuna musa hakan suma su sani.

Femi Adeshina da ya fidda sanarwar ya ce kalaman Buhari sune jawabin da yayi a lokacin da yake amsar bayanai daga shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, a lokacin da ya ziyarci shugaban kasa a Aso Rock.

Yakubu bayyana wa shugaban kasa yadda wasu ke bin ofisoshin hukumar suna babbakewa.

Ya gaya masa cewa, zuwa yanzu an ko e ofisocin hukumar da dama a kasar nan.

Buhari ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ganin an yi zabe, yana mai fayyace masa cewa ba za su ba wani dama da zai yi amfani da shi ya ce wai ko kila suna so su kara wadin mulkin su ne bayan 2023.

” Mun gano yanzu cewa tabbas akwai wadanda ke son suga ba mu yi nasara ba a gwamnati na mu, wato mun fadi warwas, su sani ba zasu ga haka ba. Muna nan muna sane da su kuma za su gani a kwanon tuwon su.

” Najeriya ta shiga bakin mutanen duniya, ita ce dai kullum ba bu zaman lafiya. Ba mu san abinda suke so ba masu yi mana wadannan kulle-kulle amma, aski ya riga ya zo gaban goshi, ido sai ya raina fata, nan ba da dadewa ba. Ai mun daga musa kafar ya isa haka, saboda haka su kwana da shiri tun da wuri.

Shi ko farfesa Yakubu a karshe cewa yayi wadanda ke aikata wannan munanan abubuwa da dangar suke yi kawai don su kawo rudani a kasa, zaman lafiya ya gagara kwata-kwata, shikenan burin su ya cika.