Ambaliya: ‘Ku daina zubar da shara a magudanan ruwa’~ Gwamnan Neja

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamna jihar Neja Abubakar Sani Bello ya buƙaci al’ummar jihar da su guji zubar da shara a magudanan ruwa domin kaucewa ambaliya, a ci gaba da samun ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a jihar ta Neja.

Cikin wata sanarwa da Sakatariyar watsa labaran gwamnan Mary Noel-Barje ta fitar, ta ce Gwamna Sani Bello ya bayyana hakan ne a yayin da ya je duba wasu hanyoyin ruwa dake cikin garin Minna, fadar jihar.

Ambaliya: ‘Ku daina zubar da shara a magudanan ruwa’~ Gwamnan Neja
Buhari ya gana da Sheikh Ɗahiru Bauchi a Abuja

Ya ce yin taka-tsantsan ya zama dole don gujewa hatsarin da mutum ke jawowa.
A cewarsa, ya kamata mutane su guji zubar da shara cikin magudanan ruwa saboda babban abin da ke taimakawa ambaliyar ruwa kenan a jihar.
Ya kuma yi kira ga ƴan jihar da su guji yin gine -gine akan hanyoyin ruwa.
Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Muhalli da ta tabbatar da cewa an kwashe shara da aka zubar a cikin magudanan ruwa yayin da ya yi ƙira ga al’umma, musamman matasa, da su sanya idanu a magudanan ruwan dake unguwannin su don tabbatar da ba a toshe su da shara ba.
Ya kuma ba da umurnin cewa Ma’aikatar Ayyuka ta binciko magudanan ruwa da suka lalace domin ɗaukan matakin gaggawa.

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaBuhari ya gana da Sheikh Ɗahiru Bauchi a Abuja

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce dake da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jaridu.