AMAI DA GUDAWA: Mutum 575 sun kamu a Najeriya, 25 sun mutu cikin wata ɗaya

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 575 sun kamu da cutar amai da gudawa sannan ana zaton cutar ta yi ajalin mutum 25 a jihohi 16 daga ranar 4 zuwa 31 ga watan Yuly.

Hukumar ta ce an samu karin kashi 18% a yaduwar cutar a watan Yuly fiye da watan Yuni inda a watan an samu mutum 473 ne suka kamu da cutar.

NCDC ta ce daga ranar 31 ga Yuly hukumar na zargin cewa cutar ta yi ajalin mutum 91 sannan mutum 3,610 sun kamu da cutar a jihohi 31.

A jimla jihohi 10 da suka hada da Taraba, Cross River, Katsina, Borno, Kano, Ondo, Zamfara, Bayelsa, Bauchi da Adamawa na da kason kashi 87% na yawan mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya a shekaran 2022.

Yaduwar cutar

Hukumar ta ce mutum 575 ne suka kamu da cutar a watan Yuly a jihohi 16 a kasar nan.

Jihar Borno dake da mutum 160, Katsina-171 da Kano-125 na daga cikin jihohin da suka fi fama da cutar a Najeriya.

Sannan jihohin Bauchi – 62, Kaduna-14, Sokoto- 12, Zamfara -11, Filato- 11, Yobe -1, Bayelsa -1, da Jigawa-1.

Sauran jihohi da cutar ta bullo sun hada da Gombe -3, Abia-1, Benue -1, da Kebbi-1.

A watan Yuly a jihohin Borno, Bauchi, Kano da Katsina na da kason kashi 175% a yawan mutanen da suka kamu da cutar sannan mutum 10 sun mutu a wadannan jihohi.

Cutar Amai da gudawa

Cutar amai da gudawa cuta ce da ake kamuwa da ita idan ana amfani da ruwa mara tsafta ko ana zama a muhallin da bashi da tsafta ko rashin wanke hannu bayan an kammala amfani da ban daki.

Alamun cutar sun hada da zazzabin, jiri, amai da gudawa, suma da sauran su.

Ga abubuwa 10 dake haddasa barkewar cutar a kasar nan

1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.

2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.

3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.

4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.

5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.

6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.

7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.

8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.

9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.

10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.

Hanyoyin Kare kai daga kamuwa da Kwalara

1. Tsaftace muhalli.

2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.

3. A guji yin bahaya a waje.

4. Amfani da tsaftattacen ruwa.

5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.

6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.

7. Yin allurar rigakafi