Akwai isassun likitoci a Najeriya – Inji ministan Kiwon Lafiya

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya tabbatar cewa akwai isassun likitoci a Najeriya kuma gwamnatin tarayya za ta yi kokarin maya gurbin likitocin da suka daina aiki ko suka fice daga kasar.

Ehanire ya fadi haka a taron da yayi da manema labarai a Abuja ranar Talata.

Ministan ya kara da cewa babu wani takunkumin hana daukar ma’aikata likitoci da sauran ma’aikatan lafiya da aka saka a kasar nan amma tunda ma’aikatan gwamnati ne akwai ka’idojin da ya kamata a kiyaye kafin a dauki mutane aiki.

“Muna samun korafin cewa akwai likitocin da suke barin aiki amma kasar nan na samun sabbin likitoci 2,000 zuwa 3,000 duk shekara sannan adadin yawan likitocin da suke barin aiki basu dara 1,000 ba.

“Matsalar ita ce dokokin daukar ma’aikatan gwamnati da ya kamata a kiyaye sune ba a kiyaye wa.

Ministan ya ce ma’aikatar lafiya za ta hada hannu da hukumar ma’aikatan gwamnati domin fito da tsarin daukan ma’aikatan da idan likita ko ma’aikaciyar jinya suka bar aiki za a iya maya gurbin su cikin dan kankanen lokaci.

“Yin haka zai taimaka wajen kawar da matsalar karancin ma’aikatan lafiya a kasan nan.

“Wannan tsarin da za a shigo da shi shugaban hukumar ma’aikatan gwamnati ta ce zai taimaka wajen hana daukar ma’aikatan da ba a bukata a kasar.