Akwai akalla yara kanana sama da miliyan 2 da ba a taba yi musu allurar rigakafi ba a Najeriya – UNICEF

Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya UNICEF ya bayyana cewa an gano yara kanana akalla miliyan 2.3 da basu taba yin allurar rigakafi ba daga shekarar 2019 zuwa 2021.

Asusun ta ce zuwa yanzu akwai yara kanana miliyan 67 da basu yi allurar rigakafi a duniya ba inda a ciki akwai yara miliyan 48 da basu taba yin allurar rigakafi ba daga shekarun 2019 zuwa 2022.

“Baya ga yara miliyan 68 din da basu yi allurar rigakafi ba an kuma gano cewa yi wa yara kanana allurar rigakafi ya fara yin kasa a kasashe 112 a duniya.

“Matsalar rashin yi wa yara allurar rigakafi ya fi shafar yaran da aka haifa gab da bullowar ko bayan bullowar cutar Korona.

Jami’in lafiya na UNICEF Eduardo Celades ya ce Najeriya ita ce kasa na biyu baya ga India a jerin kasashen duniya da suka fi yawan yaran da basu yi allurar rigakafi ba.

“A shekarar 2021 Najeriya ta samu yawan yaran da suka kamu da bakon dauro fiye da yawan da aka samu a shekaran 2020.

Lokaci yayi da ya kamata a dauki tsauraran matakan da za su taimaka wajen ganin an yi wa kowani yaro allurar rigakafi.

Celades ya ce tsoran samun matsalolin da ake samu bayan an Yi allurar rigakafi, rashin amincewa da gwamnati, rashin ingantattun wurin ajiye maganin rigakafin, rashin wayar da kan mutane, Nisan wurin yin allurar rigakafin da sauran su na daga cikin matsalolin dake sa har yanzu ake samun yaran da ba su yi allurar rigakafi ba.