Akalla mutum sama da biliyan ɗaya ne ke busa sigari a duniya – Sakamakon Bincike

Sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa an samu karin mutane da dama da suka tsunduma shan taba gadan-gadan a duniya.

Sakamakon binciken ya nuna akalla mutum miliyan 8 sun mutu a dalilin busan taba sigari a shekarar 2019 sannan daga shekarar 1990 zuwa 2019 mutum biliyan 1.1 ne busa ta a fadin duniya.

Masu gudanar da bincike dake ‘Institute for Health Metrics and Evaluation’ suka gudanar da binciken a kasashe 204 na duniya kuma suka gabatar da wannan sakamakon bincike.

Jagoran binciken Marissa Reitsma ta ce binciken ya nuna cewa matasa tun suna shekara 15 suke fara busa taba sigari sannan kafin su kai shekara 25 sun zama riƙaƙƙu ƴan taba.

Marissa ta ce ƙaruwan yawan mutane a duniya da rashin mai da hankalin gwamnati wajen hana mutane busa taba sigari na daga cikin matsalolin da ya sa ake samun masu ƙaruwar masu shan taba.

“Bincike ya nuna cewa a shekarar 2019 kuma a dalilin busa taba sigari mutum miliyan 1.7 sun kamu da cututtukan dake kama zuciya, mutum miliyan 1.6 sun kamu da matsalar toshewar magudanar jini zuwa zuciya, mutum miliyan 1.3 sun kamu da cututtukan dake kama huhu musamman cutar dajin dake kama huhu sannan mutum miliyan ɗaya sun mutu a dalilin shanyewar ɓangaren jiki.

“Bincike ya kuma nuna cewa taba sigari na rage akalla shekaru 10 daga cikin yawan shekarun da mutum ya kamata ya yi a duniya.

Najeriya

Sakamakon binciken da cibiyar binciken tattalin arzikin Afrika (CSEA) ta gudanar ya nuna cewa a duk shekara taba sigari na yin ajalin mutum 28,876 a Najeriya.