ABUJA: An cafke masu gadin da suka yi wa ɗan sanda dukan tsiya yayin ya zo kama mai laifi inda suke gadi

Ƴan sanda sun kama wasu masu gadi biyu da suka ci zarafin dan sanda a Abuja.
A ranar Juma’ar makon jiya ne Kotun Grade 1 dake Kado Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta gurfanar da wasu masu gadi biyu da suka ci zarafin wani dan sanda.
Kotun ta gurfanar da Nevkaa Terhenem da Titus Istifanus dake aikin gadi a Kamfanin ‘ Spytech Security Organisation’ bisa laifufuka hudu da suka hada da hadin baki, daure jami’in tsaro ba bisa ka’ida ba, hana ma’aikacin gwamnati gudanar da aikinsa, cin zarafin ɗan sanda dake sanye da kayan aiki.
Ɗan sandan da ya shigar da kara Stanley Nwafoaku ya ce sifeto Shaibu Omachonu dake aiki da ofishin ‘yan sanda dake ‘Life Camp’ ne ya kawo kara ranar 27 ga Fabrairu ofishin ƴan sanda.
Nwafoaku ya ce a wannan ranar Omachonu ya je rukunin gidajen dake Efab dake Life Camp a Abuja domin kama wani mai laifi inda wadannan masu gaji suka ci zarafinsa.
“Ko da Omachonu ya iso wurin sai masu gadin suka hana shi shiga. Daga baya suka kama shi su ka daure shi tamau sannan suka fara surfar sa, cikin ikon Allah ya samu ya kuɓuta ya arce. Amma fa ya sha kila.
Sai dai kuma bayan bayyana haka Terhenem da Istifanus sun musanta cewa sun aikata hakan.
Alkalin kotun Muhammed Wakili ya ce kowani mai gadi zai biya kudin belin naira 100,000 sannan kowannen su zai gabatar da shaida a kotun.
Wakili ya ce shaidun da masu gadin za su gabatar za su gabatar wa kotun hotunan fasfo dinsu, kowani katin shaida da lambar NIN din sa sa.
Za a ci gaba da shari’a ranar 28 ga Afrilu.