ABUJA: A yi sallar Idi a masallatan Juma’ar unguwanni, babu zuwa filin Idi

Mahukuntan babban birnin tarayya, Abuja, sun hori mutane su yi sallolin Idi a masallatan juma’a da ke kusa da su, maimakon a dunguma zuwa filin sallar Idi.

A sanarwar da ministan Abuja, Mohammed Bello ya saka wa hannu, mazauna cikin gari, za su hallara masallatan Juma’a ne da ke kusa da su domin yin sallar Idi sannan kuma ayi sallah a waje ne, idan ya kama sai an yi a cikin masallaci kada a wuce mutum 50.

” Bayan haka a tabbata an saka takunkumin fuska, ana wanke hannaye da kuma bada tazara saboda kauce wa kamawa da kuma yada annobar Korona.

Jagorar limamen da suka halarci taron, Imam Adigum ya bayyana cewa lallai sun yi na’am da wannan umarni, kuma za su gargadi masallata su bi doka da aka saka domin kare kai daga Korona.

” Kowani fanni akwai kwararru, abin da masana kiwon lafiya suka ce shine za a yi. Za mu doka domin Lafiyar mu.

Haka kuma a jihohi da dama gwamnatoci da masarautu sun janye shagulgular Sallah a jihohi da masarautun su.

Idan ba a manta Kwamitin Korona ta saka dokar hana walwala daga karfe 12 na dare a fadin kasar nan har zuwa 4 na asuba. Sannan kuma ta bada umarnin kada a bude gidajen holewa da kyma duk wuraren da ake taruwa da yawa a lokacin bukukuwan sallah da bayan haka.

Kasashen Indiya Turkiyya da Birazil sun fada cikin halin kakanikayi a dalilin barkowar Korona a kasashen su.

Mutum sama da 4000 sun rasu a kasar Indiya a cikin rana daya bayan sun kamu da Korona.