A yi Hattara da ‘Yan Damfara: Kamfanin Foodco ba ya baiwa kwastamomin sa kyartar Kudade – Binciken DUBAWA

Zargi: Wani labari da ake yadawa a shafukan WhasApp na bayanin wai domin bukukuwan cika shekaru 40 da yin kasuwanci, kamfanin Foodco a Najeriya na baiwa kwatamominsa kyuatar kudi har naira 30,000.

Wannan labari da ake ta bazawa a shafukan sada zumunta ya bayyana cewa wai domin karrama kwastamomin dake hulda da kamfanin, zai baiwa wa mutane naira 30,000 kyauta wai don murnar cika shekaru 40 kamfanin na kasuwanci a Najeriya.

Mutane da dama sun rika watsa labarin a shafukan su na WhatsApp sannan suna gaya wa mutane su ziyarci shafin shagon kamfanin a yanar gizo sannan su amsa wasu gajerun tambayoyi sannan su saka labari a wasu dandali akalla guda biyar da abokan su 20 a manhajan WhatsApp. Idan har suka aikata haka za su sami kyautar naira 30,000.

Tantancewa

Dubawa ta ziyarci shafin kamfanin Foodco domin ta tantace gaskiyar wannan tallar da ake yi. Shafin Tiwita na kamfanin mai suna FoodCo Nigeria, ko daya bai nuna alamu ko bayani game da kudin da ake cewa wai kamfanin yayi alkawarin baiwa jama’a ba.

Haka nan ma a shafin kamfanin na Facebook babu wani labarin da ya yi magana akan haka. Hasali ma ranar alhamis 9 ga watan Satumbar 2021, kamfanin ya wallafa gargadi game da tallar inda tabbatar cewa labarin karya ne wato “Fake news.”

Mun tuntubi kamfanin ta wannan lambar ta WhatsApp +2349065050081 wanda muka gani a shafin kamfanin wato Foodco Nigeria, inda muka sami sakon da ya kara tabbatar mana cewa labarin karya ne, ya kuma ce mu yi watsi da wannan labari.

Mai binciken wannan labarin ya tuntubin kamfanin ta hanyar email ta adireshin care@foodco.ng wanda suka sanya a shafinsu na intanet.

Wata mai suna Adenike ta amsa tambayar da muka tura zuwa adireshin, ga kuma kadan daga cikin abin da ta bayyana mana:

“lallai an ja hankalinmu zuwa shafin intanet din da ke bayanin bayar da ladan kudi a matsayin daya daga cikin shirye-shiryen mu na bukin cika shekaru 40 da kasuwanci a Najeriya. Muna sanar da ku cewa Foodco ko daya ba shi da wannan shiri a wannan lokacin. Kuma ba mu da wata alaka da haka, damfara ce kawai.

A Karshe

Kamfanin Foodco ya karyata labarin cewa suna baiwa kwastamominsu kyautar kudi. Dan haka karya ne, kuma tarko ne aka dana domin a damfari mutane.