A KIMTSA. A SHIRYA. A YI TANADI: Zazzafar korona ta tarwatsa ɗaliban Jami’ar Legas zuwa gida

Mahukuntan Jami’ar Legas da ke Akoka, sun bada umarnin gaggawa cewa dukkan ɗaliban da ke kwana makarantar tare da masu yin je-ka-ka-dawo sun hanzarta ficewa daga makarantar.

Sanarwar wadda aka fitar a ranar Laraba ɗin nan, ta ce hakan ya zama dole bayan da Majalisar Ƙolin Jami’ar ta yi wani taron gaggawa, domin nazarin fantsamar zazzafar korona ‘yar zango na uku a cikin jami’ar.

Mahukuntan jami’ar sun ce kowa ya gaggauta arcewa zuwa gida, kuma a yi shirin fara ɗaukar darussa daga gida a ƙarƙashin tsarin karatun daga nesa-nesa, wato ‘virtual lectures’.

Wakilin mu ya kira lambar Mataimakin Jami’in Yaɗa Labarai na Jami’ar Legas, Nonye Oguama domin jin ƙarin bayani daga bakin sa, amma bai ɗaga waya ba.

An tuntubi Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Jami’a Reshen Jami’ar Legas, Dele Ashiru, kuma ya tabbatar da labarin rufe jami’ar, ya ce gaskiya ne.

“Ka ga hakan ya tabbatar da ƙorafin da na sha yi a baya cewa Gwamnatin Tarayya ba ta ɗaukar ƙwararan matakan kariyar kamuwa ko baza korona a jami’o’i.

“Ba a ɗaukar matakai a jami’o’i kamar yadda ake ɗauka a ofisoshin manya. Kuma hakan ya na nufin gwamnati ba ta damu da inganta fannin ilmi a ƙasar nan ba.” Inji shi.