2023: Za mu amince da jam’iyyar da ta nemi mu ƙulla ƙawancen cin zaɓe – NNPP

Yayin da zaɓen 2023 ke matsowa, Shugaban Jam’iyyar NNPP na Ƙasa, Rufai Alƙali ya bayyana cewa su na marhabin da duk jam’iyyar da ke neman su ƙulla ƙawancen lashe zaɓe.
Rufai wanda tsohon Mashawarcin Harkokin Siyasa ne na tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana haka a Legas, a wani taron manema labarai da ya shirya, a ranar Laraba.
Alƙali ta ce NNPP ba ta ƙyamar duk wanda zai zo ya haɗa zumuncin ƙarfi wuri guda domin a samu nasara.
“Duk wata jam’iyyar da ke son haɗa ƙarfi da NNPP ƙofa a buɗe ta ke, kuma dole sai kowane ɓangare ya san matsayin sa, kuma tilas ya kasance irin fahimta da manufofin mu na ciyar da ƙasa gaba sun yi iri ɗaya ko kamanceceniya da juna.
“Saboda a dokance dukkan jam’iyyu daidai su ke da juna, babu wani fifiko.
“Idan mu na magana kan makomar Najeriya kuma kyakkyawar makoma, to wannan shi ne matsayar mu.” Inji Alƙali wanda ya taɓa riƙe muƙamin sakataren yaɗa labarai na PDP.
Sai dai kuma Alƙali ya gindaya sharuɗɗan cewa duk wata jam’iyyar da ke neman ta yi ƙawance da NNPP, to kada ma ta je masu da buƙatar cewa ɗan takarar su Rabiu Kwankwaso ya janye ya bar wa na su kujerar takarar shugaban ƙasa.
I makonnin baya duk wani ƙoƙarin ƙulla ƙawance tsakanin NNPP da LP ta Peter Obi bai yi nasara ba, bisa hasashen cewa Kwankwaso da Obi kowa ya ƙi yarda ya haƙura da takara ya bar wa ɗayan.
Wannan ce ta sa kowanen su bayan shafe kwanaki ana tattaunawa, a ƙarshe ya fitar da sunan ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na sa.
Alƙali ya ce ƙawance tsakanin jam’iyya kuma mataki mataki ne. Zai iya tsakanin majalisar jiha ko tarayya ko ta dattawa, ko iyakar zaɓen gwamnoni ko kuma har zuwa zaɓen shugaban ƙasa.
“Saboda a siyasa sai da mai kama ake yin ƙota. Da mai kamar zuwa ake yin aike.” Inji Alƙali.
Ya ce bai kamata Najeriya ta sake yin sakaci ta tabka kuskuren sake zaɓen waɗanda ba su cancanta ba.
Ya ce NNPP jirgin ceton al’umma ne, wadda ya wajaba kowa ya shiga domin hana ambaliyar ruwa nutsewa da shi da kwale-kwalen da ya ke ciki.