2023: Ya mutan Adamawa, ga Tinubu ga Binani na kawo muku su – Shelar Buhari a Yola

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hori mutanen jihar Adamawa su zaɓi dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, da Aishatu Binani kujerun shugaban kasa da gwamnan jihar Adamawa.
Dubban magoya bayan jam’iyyar APC ne suka halarci wannnan gangami.
A jawabin da yayi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga mutanen jihar Adamawa su zaɓi Binani mace ta farko da za a zaɓa gwamna a kasar nan idan Allah ya yarda.
Jihar Adamawa dai ita ce jihar ɗan takarar shugaban kasa na PDP wato Atiku Abubakar, sannan kuma gwamnan dake kan mulki, Ahmadu Fintiri shima ɗan PDP ne.
Binani na talakawa
Ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa ta jam’iyyar APC, Aisha Binani ta bayyana cewa abinda ya sa talakawa ke ƙaunarta a jihar Adamawa shine saboda kula da su da take yi.
Binani ta bayyana haka a lokacin da take amsa tambayar manema labarai a fadar shugaban kasa yayi kammala ganawa da shugaba Buhari da ta yi.
Binani ta ce ta ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ne don ta gode masa bisa amsa gayyatar da yayi na halartar gangamin kaddamar da kamfen din ta na gwamna wanda za ta yi ranar 9 ga Janairu.
” Shugaba Buhari ya yi matuƙar farin cikin gani na sannan ya yi mani fatan Alkhairi, da kuma addu’ar yin nasara a zaɓe mai zuwa.
Da aka tambayeta ko me ya sa ta ke da matuƙar farin jini a jihar Adamawa fiye da sauran jigajigan jihar musamman ƴan siyasa Binani ta ce ” Babu abinda na sa a gaba a rayuwata baya ga taimakon talaka da miskini. Idan ka tafi jihar Adamawa ka ambaci sunan talaka, toh abu na biyu da za a kira shina sunana ‘ Binani’.
” Kafin in zama sanata sai da nayi wakilci a majalisar wakilai ta tarayya, mutane sun shaida wakilci na, sun ce basu taɓa samun wakili da ya kula da su irin yadda na yi ba.
” Haka ko yanzu da nake wakiltar su a majalisar dattawa, maganar dau ɗaya ce dai, ba a taɓa yin kamata ba a majalisar daga jihar ba.
Sabon da haka ne ko yanzu mutane sun san cewa idan na zama gwamna za su wataya su kwankwaɗi romon dimokuraɗiyyar da ba su taba samun irin sa a jihar ba.