2023: Aisha Buhari na so kowace jam’iyya ta tsayar da mace takarar mataimakiyar shugaban ƙasa

Uwargidan Shugaban Ƙasa, A’isha Buhari ta yi kira ga dukkan jam’iyyun da zasu kafsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, su tsayar da mace a matsayin ‘ysr takarar muƙamin Mataimakiyar Shugaban Ƙasa.
A’isha ta yi wannan kalami ne a lokacin da ta ke jawabi wurin taron buɗe-baki da ta gayyaci ‘yan takara daga jam’iyyu daban-daban.
An yi taron a ranar Asabar da dare, a Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja.
Taron dai an shirya shi domin neman lada alfarmar watan Ramadan, inda ‘yan takara daban-daban za su gana da juna, su ƙara danƙon zumunci da ƙaunar juna, a ƙoƙarin ƙara gina ƙasa.
A’isha ta ce adalcin da ya kamata a yi wa mata a yanzu, shi ne a ƙara masu damar shiga cikin gwamnati da shugabancin manyan muƙamai.
“Lokaci ya yi da za a fara bai wa mata muƙamai, ana ba su guraben mataimakin shugaban ƙasa, mataimakin gwamna, majalisa har ma da ƙananan hukumomi.
“Yayin da mu ke ta tseren kaiwa ga zaɓen 2023, ina da yaƙinin cewa Najeriya za ta ci gaba da bunƙasa sannu a hankali a bisa turbar dimokuraɗiyya.” Inji A’isha.
Daga nan sai ta yi kira ga duk ‘yan takarar shugaban ƙasa su maida hankali wajen ƙarfafa haɗin kan Najeriya, ƙarfafa zumunci da kusantowar juna.
Ta tunatar da su cewa zaɓen 2015 wani al’amari ne muhimmi a tarihin Najeriya.
“Saboda shi zaɓen 2015 ba a tsaya ja-in-ja har aka je kotu ba. Haka ra’ayoyin jama’a ma duk a ɓangare ɗaya suka karkata, babu wata tankiya.
“Saboda haka babbar kyautar da ‘yan Najeriya za su yi wa iyalan Shugaban Ƙasa shi ne a gudanar da zaɓe sahihi, kuma karɓaɓɓe a cikin Najeriya da duniya baki ɗaya, a 2023.”
Daga nan kuma ta yi kira a guji tashe-tashen hankula musamman lokutan yaƙe-yaƙen neman zaɓe.
Da ya ke jawabi, Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, wanda tsohon gwamnan Edo Oserheimen Osunbor ya wakilta, ya yi kira ga dukkan ‘yan takarar su yi siyasa ba da gaba ba.
Shi kuma Bola Tinubu ya bayyana godiya ga A’isha Buhari da ta yi ƙoƙari har ta haɗa gungun mabambanta ra’ayi a wuri ɗaya domin a ƙarfafa soyayya da kishin ƙaunar ƙasa da haɗin kan al’ummar da ke cikin ta.
Cikin waɗanda ke wurin har da gwamnan Ebonyi Dave Umahi, Wanda shi ma ɗan takara ne.