Wata mata mazauniyar unguwar Rigasa dake cikin garin Kaduna ta maka mijinta a kotu ta na rokon kotu ta tilasta mijinta ya biya ta kuɗin da ta bashi a lokacin da yayi mata alkawarin zai kaita kasar Saudiyya.
Karima Nuhu mai shekar 45 ta shaida wa alkali cewa tun bayan auren ta da mijinta Musa Falalu ya banzatar da ita ko abinci baya bata.
” Tun bayan auren mu, ina gani wata biyu kacal Falalu ya ciyar da ni. Daga nan ya kama gaban sa.
” Falalu ya fadi mani cewa ya rasa aikin sa na tukin mota, amma ya samu wani aiki a Saudiyya. Kuma tare ma za mu tafi can abin.mu.
” Haka yasa na rika dankara masa kuɗi na har bashi na ci ina bashi don zai kai Saudiyya. Amma kuma daga baya sai ya sake ni.
Falalu ya ƙaryata duk abinda karimanta faɗi yana mai cewa ba matar sa ba ce yanzum
Sai dai kuma alkali ya tambayeta ko tana da shaidun da za ta gabatar domin a bi mata hakkinta kamar yadda ta ke buketa.
Karima dai a karshe ta ce ba ta da shaida, tsakaninta da mijinta ne kawai suka yi abin su sai kuma Allah dake ganinsu.