Ƴan Najeriya 60 da suka dawo daga kasar Ukraniya sun yo wa Najeriya tsarabar Korona

Alkaluman yaduwar cutar Korona da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa mutum 118 ne suka kamu da cutar a kasar a wannan rana

Hukumar ta ce an samu ƙarin yawan masu ɗauke da cutar ne bayan an gano matafiya 60 da suka dawo daga ƙasar Ukraniya dukkan su ɗauke da cutar.

Bayan su kuma sai waɗanda suka kamu da ita a garin Abuja

A ranar Litini mutum biyu me kada suka kamu da cutar sannan babu Wanda ya mutu.

NCDC ta ce tun bayan bullowar korona a shekaran 2020 wannan shine mafi kankanta yawan mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya.

Zuwa yanzu gwamnati ta dawo da ‘yan Najeriya 772 daga kasar Ukraine a jirgin saman Max Air da Air Peace.

Yaduwar cutar

Alkaluman gwajin cutar na ranar Talata sun nuna jihar Legas ita ce kan gaba wajen yaduwar cutar da mutum 49.

Jihar Rivers ta samu mutum daya da ya kamu da cutar.

Zuwa yanzu cutar ta yi ajalin mutum 3,142 sannan mutum 254,777 ne suka kamu da cutar.

An sallami mutum 249,209 sannan mutum 2,311 na dauke da cutar a kasar nan.

Legas- 98,957, Abuja-28,439, Rivers- 16,584, Kaduna- 11,224, Filato- 10,247, Oyo- 10,215, Edo- 7,694, Ogun- 5,810, Delta- 5,364, Ondo-5,173, Kano- 4,972, Akwa-Ibom- 4,657, Kwara- 4,579, Gombe- 3,307, Enugu- 2,952, Anambra- 2,825, Nasarawa- 2,729, Imo-2,558, Katsina- 2,418, Abia- 2,116, Benue- 2,129, Ebonyi- 2,064, Ekiti-1 1,982, Bauchi- 1,939, Borno- 1,629, Taraba- 1,473, Bayelsa- 1,312, Adamawa- 1,203, Niger- 1,148, Cross Rivers – 823, Sokoto- 817, Jigawa- 667, Yobe-564, Kebbi-480, Zamfara- 375 da Kogi-5